Thursday, 12 July 2018

- Mata a yankin arewacin kasar Iraki na neman mazajen aure ruwa a jallo,

Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo
Mata a yankin arewacin kasar Iraki na neman mazajen auren  ruwa a jallo.

A birni mafi girma na biyu a kasar ta Iraki, yawan mata marasa aure na cigaba da karuwa babu kakkautawa, musamman ma wadanda suka bawa shekaru 20 baya, yayin da mazajen aure suka zamo tamkar dinare a yankin.

Wannan lamarin wanda ya kunno kai saboda gudun hijarar da mafi yawancin mazajen yankin suka yi zuwa kasashen ketare, hakan yayi matukar tayar wa da matan yankin hankali.

Bincike ya nuna cewar kashi uku cikin hudu na mazan yankin sun bar kasar ga baki daya, don guje wa matsin lamba da haramtacciyar kungiyar DAESH take yi musu.
A yanzu haka dai, matan yankin Mosul na ci gaba da neman mazajen aure ruwa a jallo.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: