Monday, 9 July 2018

Ina da shekara 13 akayi mani auren fari, kuma yanzu haka inada 'Da - inji Maryam Gidado.

Shahararriyar jarumar nan da tauraronta ke haskawa a masana’antar Kannywood, Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban ta yi tsokaci akan wani babi daya shafi rayuwarta.

A cewar Maryam bazawara ce ita domin ta taba yin aure har sau biyu. Jarumar ta bayyana cewa anyi mata auren fari tana da shekaru 13 a duniya kasancewarta Bafulatanar asali.

Ta kuma ta haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurar da ita ga mijin nata na fari.

Ta kuma kara yin aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.


Daga karshe Maryam ta jaddada cewa burin ta ya cika a yanzu musamman a harkar fim sai dai kawai addu'an Allah ya bata miji nagari ta raya Sunnah.

Duk wanda yake  ciki yayi bayani...

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: