Monday, 9 July 2018

Kyakyawar alaka ta kullu tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau (Gakuma kadan daga cikin Hotunan da suka dauka tare)

Rahotanni dake zuwa mana daga masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood ya nuna cewa Kyakyawar alaka ta kullu tsakanin jaruman Fim Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau sosai a yanzu.

Hakan ya biyo bayan rashin fahimta da zafaffiyar gaba da ta shiga tsakanin jaruman biyu.
A baya jaruman sunyi ta musayar zafafan kalamai a tsakaninsu inda rashin jituwarsu ya fito karara a bainar jama’a.

Har ana zargin hakan ya kasance ne sanadiyar kokarin dishewar tauraruwar Nafisa dake haskawa bayan shigowar Rahma masana’antar.

Bisa ga hasashen jama’a wannan ne ya sanya kishi da kiyayya a tsakanin jaruman.sai dai komai ya daidaita a yanzu, domin an gano jaruman a inuwa daya cikin farin ciki da annashuwa.

Ga kadan daga cikin irin hotunan dasuka dauka a wannan lokacin





SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: