Shi dai wannan makwabci na Malam Kabiru Gombe yayi kararsa ne gaban kotu kan zarginsa da take akan hakkin makwabtaka, kamar yadda ya shaida ma alkalin kotun, Sarki Yola.
makwabcin yana fadin wai Kabiru Gombe ya sanya wasu waga wagan Tagogi a sabon gidansa daya gina a unguwar Sabuwar Gandu, inda makwabcin ke zarginsa da samun damar liken matayensu.
Makwabcin ya kara da cewa “Wannan Malamin ya gina manyan tagogi, sa’annan ya sanya musu bakaken gilasai, ta yadda shi zai iya ganin jama’a, amma mu ba zamu gan shi ba.”
Wannan makwabci dai ya cigaba da shaida ma kotu cewar tun lokacin da aka fara ginin gidan suka janyo hankalin Malamin, amma bai dauki wani mataki game da hakan ba.
Sai dai lauyan Malamin Ishaq Adam Ishaq ya bayyana ma kotu cewar ba wani bane ke damun wannan makwabci illa bakin ciki da hassada da suke yi da Malamin sakamakon daukaka da Allah yayi masa.
Daga karshe dai Alkali Sarki Yola ya aika da jami’an kotu da su tafi su gano masa yadda wadannan tagogi suke, sa’annan su kawo masa rahoton abinda suka gani, bayan nan sai a cigaba da sauraron karar.
0 comments: