Munyi Nadamar Shiga Kwankwasiyya, Cewar Magoya Bayan Kwankwaso A Jihar Jigawa Da Suka Yi Bikin Kone Jar Hular Kwankwaasiyya
Magoya Bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, A Karamar Hukumar Ringim Dake Jihar Jigawa, Sun yi Bikin Kone Jar Hular Kwankwasiyya, Bayan Da Suka Samu Labarin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar APC Zuwa Jam'iyyar PDP.
Mai Magana Da Yawun Matasa Kwamarad Mustapha Fatoma Ringim, Ya Bayyanawa Wakilin RARIYA Cewa Kwankwaso Ya ci Amanar su Kuma Sun yi Nadamar Bin shi A Siyasance, Wannan Dalilin Ne Ya sa Suka Bankawa Jajayen Hulunansu Wuta.
Sannan Kwamarad Mustapha Fatoma Yace Suna Nan Daram A Cikin Jam'iyyar APC.
Monday, 30 July 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: