Wednesday, 8 August 2018

Duniya Ba Wajen Zama Ba: Ba duka ba zagi wani mutumi ya fadi matacce a tasha (Hoto)

Mutuwa rigace ba ta fita, kamar yadda wani mawaki yaka fadi, kuma dama idan ajali yayi kira, ai ko ba cuta sai an je, wannan shine kwatankwacin lamarin da ya faru a jihar Legas, inda wani mutumi ya fadi matacce babu sididi babu sadada.

Arewarmu.com ta ruwaito wannan mutuwar fuju’a ta faru ne a tashar Mota dake Orile Iganmu a ranar Talata, 7 ga watan Agusta, inda rahotanni suka bayyana cewa mutumin ya tafiya ne kawai ya fadi, ko da aka duba tuni ya rigami gidan gaskiya.

Wani mai shago dake kusa da inda lamarin ya faru, Yinus Olayiwola ya bayyana cewa yana shagonsa da misalin karfe 6:30 na safe ya hangi mutumin yana ta rawar sanyi sakamakon ruwan sama dake dukansa.


Shima wani mazaunin yankin da lamarin ya faru a idonsa, Bamidele Adejoke ya musanta jita jitan cewa mutumin mahaukaci ne, inda yace da hankalinsa, kawai dai rashin lafiya ne ya addabe shi, don haka yayi kira ga jama’a da su dinga kulawa da lafiyarsu.

Sai dai Bamidele ya bayyana bacin ransa da yadda har bayan awanni takwas hukumomi basu dauke gawar mamacin ba, inda yace hakan cin mutuncin mamacin ne.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: