Wednesday, 8 August 2018

Kannywood: Jaruma Saratu Gidado Daso Ta Saki Zafafan Hotunanta Tare Da Mijinta

Fitacciyar jarumar nan ta wasan Hausa a masana'antar fim ta Kannywood, Hajiya Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta saki zafafan hotunan ta tare da mijin ta.
Jarumar dai tayi fice sosai a masana'antar musamman ma a wajen rawar ta da take takawa ta tsiwa da fada a cikin fina-finan ta da dama.

A baya ne dai jarumar ta sake yin aure inda kuma ta bayyana a cikin wata fira da tayi da 'yan jarida ta ce ita ba zata dena yin fim ba duk da kasancewar tayi Auren.

To yanzu haka dai jarumar na cigaba da fito a fina-finai duk da dai za'a iya cewa ta rage fitowa watakila saboda wasu harkokin na ta na daban dake da alaka da auren nata.

Ga dai wasu hotunan nan nata:

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: