Allah mai iko, wasu na tsananin son samun haihuwa wasu kuma ya basu suna jefarwa – Wata mata ta ajiye Jaririnta ta arce a Kaduna – Har ya zuwa yanzu ba’a kaiga gane ko wacece ba An tsinci wani kyakkyawan jaririn yaron a bayan wani kango daidai da babbar makarantar Sakandire ta Higher Islam dake Tudun Wada Kaduna. Kalli hotan kyakkyawan jaririn da aka jefar a Bola Bayanai sun tabbatar da cewa wata mata ce tazo da cikin mota kirar Golf sannan ta ajiye jaririn kana suka gudu a guje.
Yanzu haka dai an bar ‘yan wadanan unguwa da sallallami da salati, yayinda wasu suke kokarin sanar da hukuma. Ko da a watan da ya gaba sai da aka kama wata yarinya da take yunkurin kashe jaririnta bayan da ta ajiye shi a karkashin Tirela da zimmar ta tatsile shi. Haka zalika a cikin dai watan da ya gabata ma a jihar Legas aka wayi gari da ganin wata jaririya da yasar a cikin bola

0 comments: