Thursday, 9 August 2018

Premier League Transfer :-Kai Tsaye zaka samu cikakkun Labarain Transfer na Premier League


Kocin Man Utd Mourinho "ba shi da kwarin gwiwa" game da sayen 'yan wasa

Chelsea ta dauki aron Kovacic daga Real Madrid, za a bayyana Courtois a Real
Wane dan wasan kulob dinka zai saya a kurarren lokaci?


Dan wasan da Man City ta rasa..
Dan wasan da Manchester City ta Rasa Boateng ya yarda ya koma kungiyar kwallon kafar Paris St-Germain, yayin da Bayern Munich ta shirya sayar da shi kan kudi fan miliyan 40.5, in ji Le Parisien

Man City ta kasa sayen dan Bayern
Manchester United ta kasa sayen dan wasan
Bayern Munich mai shekara 29 Jerome Boateng domin suna ya buga musu wasan aro ne kawai, in ji Sun .


An rattaba hannu
Domin kada a yi shakka game da sayen sabon gola, Real ta wallafa bidiyo a shafin Twitter inda Courtois yake rattaba hannu kan yarjejeniyar komawarsa Madrid......


Maguire na da kwarin gwiwar komawa Man U
Har yanzu dan wasan bayan Leicester dan Ingila Harry Maguire, yana da kwarin gwiwar komawa
Manchester United, duk da cewa an yi fatali da tyi biyun da kulob din ya yi wa dan wasanmai shekara 25, in ji Sky Sports

Sai dai kuma....
Sai dai kuma Leicester ta hakikance akan cewar ba za ta sayar da Maguire ga Manchester United ba, in ji Daily Mail .


Courtois ya kusa zama dan Madrid
Gola Thibaut Courtois ya kusa zama dan wasan Real Madrid.
Real ta nuna hoton gwaje-gwajen da ake yi wa dan wasan...


Saura sa'o'i biyar
A halin yanzu dai saura sa'o'i biyar a rufe kasuwar musayar 'yan wasa a gasar Firimiyar Ingila.
Me kake ganin kulob dinka za samu kafin a rufe kasuwar?


Man City ta sayi Daniel Arzani
Manchester City ta sayi dan wasan tsakiyar Australiya Daniel Arzani daga Melbourne City.
Dan wasan mai shekara 19 asalinsa Iran ne.


West Ham ta sayi dan wasan Arsenal
West Ham ta sayi dan kasar Sfaniya daga Arsenal kan kudi fan miliyan 4.
Dan wasan mai shekara 29 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara uku da Hammers, bayan ya shafe shekara biyu da Gunners.


Chelsea ta sayi golan Atletic Bilbao
Chelsea tsa yi Kepa Arrizabalaga daga Athletic Bilbao kan kudi fan miliyan 71 - kudi mafi yawa da aka taba kashewa wajen sayen gola, kuma kudi mafi yawa da kulob din ya taba kashewa.
Kepa, mai shekara 23, zai isa Stamford Bridge bayan an cimma sharadin fansa cikin yarjejeniyarsa .

Mounrinho ba shi da kwarin gwiwar sayen dan wasa
Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya ce shi ba shi da kwarin gwiwar sayen wani dan wasa kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar Alhamis.
Mourinho ya dade yana jaddada cewar yana son ya kara 'yan wasa gabannin kakar bana inda ya fi mayar da hankali kan sayen dan wasan baya na tsakiya.


Chelsea ta dauki aron Kovacic
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dauki aron Mateo Kovacic na tsawon shekara daya daga Real Madrid, yayin da ake tsammanin komawar gola Thibaut Courtois Marid zai tabbata ranar Alhamis.
Dan wasan tsakiya, Kovacic, mai shekara 24, ya kasance a Real tsawon shekara uku tun da ya koma kulob din daga Inter Milan.


Leicester ta sayi Benković
Kungiyar kwallon kafa ta Leicester ta sayi dan wasan baya Filip Benković daga Dinamo Zagreb.
Dan wasan mai shekara 21 wanda ya koma kungiyar kan wani kudin da a bayyana ba, ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da kulob din.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: