Monday, 13 August 2018

Uwar Jiki: Hukumar NAFDAC Ta Bukaci A Tsaftace Kayan Lambu

Hukumar dake kula da inganci abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta gargadi mutane kan amfani da wani daskararren man girki da aka shigo da shi wanda ke dauke da wani sinadarin guba dake da illa ga jikin dan Adam.


Daraktan hukumar Mojisola Adeyeye ta bayyana hakan a lokacin wani taro na musamman da aka gudanar domin wayar da kan al’umma kan illar da ke tattare da wannan man, inda ta bukaci a dawo da duk wani samfarin daskararren man da aka shigo da shi daga ranar 13 ga watan Ogustan 2016, zuwa 20 ga wantan Yunin 2018 zuwa ofishin hukumar.

Sai dai tun da farko wata hukuma dake kula da ingancin abinci ta duniya, ta gargadi hukumar Najeriya kan barkewar wata cuta a kasashen turai bayan da suka yi amfani da wannan sinadarin mai, wanda yake dauke da wannan kwayar cuta.

Hukumar NAFDAC ta ce yanzu haka tana gudanar da bincike a jihohin Lagos, da Port Harcourt da kuma babban birnin tarayya Abuja.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: