Monday, 13 August 2018

Zagin Malamai Fasikanci Ne – Inji Malam Aminu Daurawa

Cikin matsanancin bacin rai ya nufo ni yana mai gaggawa rike da asuwaki kamar zai tashi sama. Kusan a lokuta da dama idan ka gan shi a wannan yanayin addinin Musulunci aka taba.

“Wai me ya sa mutane suka lalace ba su da tarbiyya?”

Me ya faru? Na tambaye shi.

“Haka kawai sai wasu jahilan mutane su rika zagin malamai, kawai don Sheikh Daurawa bai yi magana akan bikin ‘yar Ganduje ba sai a rika zagin sa?”

Gaskiya ba daidai ba ne.

“Ta ko ina an sako Sheikh Daurawa a gaba da zagi gami da cin mutuncin bayan kuma masu zagin nasa ya fi su ALHERI a rayuwa. Malam Ibrahim Daurawa yana da ALHERI mara misaltuwa a duniyar Musulmi da Musulunci. A iya shirinsa kadai na Tambaya Mabudin Ilimi Allah ne kadai Ya san yawan mutanen da suke amfana da ilimin sa”.

Ai dole a zage shi yaya za a ce Matar aure kuma Musulma sannan Hausa/Fulani kuma yar jihar Kano kuma ‘yar Gwamnan jihar Kano ta fito daga ita sai riga ba kallabi sannan nonuwanta a waje tana tikar rawa a bainar jama’a?” Wani ya ba shi amsa.

“Abubuwa nawa ne aka yi ba aka nemi Malamai su yi magana ba sai wannan don ayi amfani da shi wajen cimma manufar siyasa? Shi fa addinin Musulunci yana da tsari ba wai kai ne za ka sa Malami a gaba ka ce ga abinda kake so yayi Wa’azi a kansa ba. Sannan kuma abubuwa nawa Malaman suka fada ba kwa aiki da su, sai yanzu da abu ya shafi siyasa za ku sa su a gaba wai dole sai sun yi magana? ”

Yanzu kana nufin abinda ta yi daidai ne?

“Ba ita ba duk wanda ya aikata mummuna sunan sa mummuna kuma ba daidai ba ne, amma kuna ina wani jahili a garin nan ya zo ya rika zagin malamai saboda sun fadawa Buhari gaskiya? Wanne mataki kuka dauka? Murna aka rika yi ana cewa ya kyauta me ya sa suka shiga siyasa?”
Gaskiya ne.

“Kawai mutane sai lokacin biyan bukatar siyasar su ya zo sai su zama masu ba wa Malamai umarni su fadi kaza da kaza. Sannan a dauka a rika sa wa a kafafen yada labarai don a ci zabe ko a kayar da wani zabe? Don haka ZAGIN MALAMAI FASIKANCI NE, kuma Wallahi mu kiyayi zagin wadanda a wajen Allah sun fi ka ALHERI”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: