Saturday, 8 September 2018

Kannywood: Adam A Zango na da saurin fushi idan ya gano ka yaudare shi - Lawal

A cikin labaran da muke kawo maku daga dandalin Kannywood, a yau NAIJ.com ta duba wani bangare na rayuwar jarumi a masana'antar shiry fina finan Hausa, wanda ya fara wannan sana'a da kida, waka, daga bisani likafarsa ta ci gaba, har zuwa yau da wasu ke masa lakabi da 'Yariman Kannywood'.
Kamar yadda kowane dan Adam ya ke da fuska biyu; fushi da dariya, haka shima jarumi Adam A Zango ya ke. Akwai abubuwa da dama da suke sanya shi farin ciki, wasu kuma su sanya shi bakin ciki. Sai dai, dole ne a samu muhimmai daga cikinsu, wadanda mutum ke harzuka matuka akansu, ko kuma ya tsinci kansa cikin matsanancin farin ciki akansu.

A bangaren Adam a Zango, ko wadanne muhimman abubuwa ne ke sanya shi saurin fushi?

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta zanda da wani dan uwan Adam A Zango, dan kasuwa kuma dan siyasa, Lawal Idiya Usman, ya bayyana manyan dalilan da ke saurin harzuka jarumin, da kuma wadanda ke sanya shi farin ciki, kasancewar sunyi kuruciyarsu a tare.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: