Saturday, 8 September 2018

Kannywood: An yi sulhu tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu

Adam Zango, na fina-finan Hausa, ya shirya da Ali Nuhu tsohon ogansa, wanda suka babe a 'yan kwanakin baya.
Shirin nasu na zuwa ne bayan da Aliyun ya ci kyautar Jarumai a taronsu na 'yan fim.

Adam Zangon, yayi jinjina ga ogan nasa, inda ya kira shi da Sarki, kuma Oga, ya kuma taya shi murnar lashe kyautar.

A shafinsa na Instagram, Adam Zango, ya wallafa hotonsa da Ali Nuhun inda ya durqusa gaba nai, ya kuma ce 'tuba nake sarki'.


Su kuma mabiya sun dauki abin da shewa, inda suka ce ai dama sun san fadan na manyan biyu na wasa ne.

Ali Nuhu dai ya zuwa yanzu bai mayar da martani ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: