Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya ce bai taba shirya fim din da ya yi amfani da fasahar kirkire-kirkire a kansa kamar Mansoor ba.
Fim din na Mansoor ya lashe lambar yabo ta fim mafi kayatarwa da aka shirya a cikin Nijeriya [rukunin Hausa] a bikin Africa Magic Viewers Choice Awards na bana, wanda aka yi a birnin Lagos ranar Asabar da daddare kamar yadda BBC ta rawaito
Fim din Mansoor, wanda jarumin ne ya shirya kuma ya ba da umarni, labari ne na wani matashi ɗan gaba-da-fatiha.
Mahaifiyar Mansoor ta yi ƙoƙarin ɓoye masa wani sirri game da asalinsa, sai dai soyayya ta sanya shi neman sanin gaskiyar al’amari.
Iyayen wata yarinyar da soyayya ta hada su a sakandare ne suka yi masa gorin asali, inda hakan ya tilasta masa katse karatu, ya bazama duniya don gano mahaifinsa.
Ali Nuhu ya shaida cewa ya yi matukar jin dadi da fim din ya yi zarra cikin sauran fina-finai.
A cewar sa, “Ina ganin Mansoor ya samu wannan nasara ce saboda bamu taba shirya fim wanda aka yi amfani da fasahar kirkire-kirkire kamar sa ba; mun kashe kudi sosai sannan mun yi amfani da na’urori na zamani wurin daukar fim din.”
Jarumin na Kannywood ya kara da cewa yanzu bai san adadin lambobin yabo da kyautukan da ya samu ba a harkar yin fina-finai, yana mai shan alwashin ci gaba da shirya fina-finai masu kayatarwa.

0 comments: