Wata matan aure mai ‘ya’ya 3, Ronke Olanrewaju, ta barazanar kashe mijinta ta hanyar saka masa guba idan har kotun al’ada ba raba auren da ke tsakaninta da mijinta ba.
Matar wadda ta bukaci kotun al’adan da ke Oja-Oba, Mapo, a birnin Ibadan, a jihar Oyo da ta raba auren da ke tsakaninta mijinta a kan zargin mijin na ta na cin zarafinta.
Ronke ta fadawa kotun cewa mijinta, Sunday Olanrewaju, yana ma ta dukan tsiya da ya same ta da maza masu siyan kayan da ta ke siyarwa inda ta kara da cewa a duk lokacin da aka shigar da ‘yan sanda cikin lamarin, sai yayi amfani da daukakar da Allah ya masa kasancewar na dan siyasa.
Ta ce, “Mai shari’a, ya taba yiwa mahaifiyar ta dukan tsiya kamar jaririyar da ya haifa. Ku raba auren da ke tsakani na da shi a yanzu ko kuma zan saka masa guba. A duk lokacin da ni ke gudanar da kasuwanci na tare da maza masu siyan kayayyaki na, ya kan ma ni dukan tsiya sai ya ce ai masoya na ne.”
Duk da haka, mijin Ronke, Sunday, ya roki kotun da kada ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa, inda ya ce matar na sa ta kasance kamar uwa a wurinsa.
Alkali kotun, Cif Henry Agbaje, ya daga ranar saurarar karar zuwa 18 ga watan Satumb, 2018.

0 comments: