Wednesday, 5 September 2018

Musha Dariya: Alhaji Da Uwargidansa A Cikin Jirgi Mai Tangarda

Wani Alhaji suna tafiya da uwargidansa a jirgin sama sai aka fara sanarwa cewa jirgi ya samu tangarda kuma duk wata dabara ta kare.

Ana tunanin nan da mintina biyar jirgin zai tarwatse saboda haka kowa yayi bankwana da abokinsa na ciki, kowa na
neman matarsa/mijinta su yafi juna sai matarsa tace don Allah ya yafeta akwai wani laifi da tayi masa a baya wanda da ya san dashi da tuni sun rabu sai yace haba dear! Ina sauran rabuwa mutuwa ta zo ai ki fadamin kawai kafin lokaci yayi…

Sai ta ce: gaskiya tun kafin ta aureshi dama ta hadu da mazaje a waje kuma har yanzu bata fasa ba tana tunanin yaransu ma uku cikin biyar ba nashi ba ne, sannan barayin da suke zuwar masa ita ce take kiran su a waya idan ya amso kudi daga banki.


Sai ya ce toh! Koma dai mene ne yanzu yaya zanyi? Na yafe miki.
Allah ya jikanmu.

Tana ce wa amin, sai aka sanar jirgi ya daidaita.

Wai in kai ne ya za ka yi?. xakaci gaba daxama da ita amatsayin mata kokuwa xaka sallameta takara gaba??

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: