Saturday, 9 February 2019

Babban Al'amari: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba

Babban Al'amari: Miji ya kashe kan sa bayan ya kwara wa matar sa ruwan guba


Wani magidanci, Daniel Okafor, mai matsakaitan shekaru ya kashe kan sa bayan an yi zargin cewar ya watsa wa matar sa wani wani ruwa mai guba a garin Nsugbe da ke jihar Anambra.

Marigayin, dan asalin garin na Nsugbe, ya hallaka kan sa ne da misalign karfe 2:30 na dare bayan ya kwankwadi ruwan gubar da ya kwara wa matar sa,

Majiyar mu ta shaida mana cewar Okafor ya fusata ne bayan ya gano cewar matar sa Paulina ta saka sunan dan su a matsayin wanda zai ci gadon gidan da ta gina,

Wani mazaunin garin Nsugbe da bai yarda a ambaci sunan sa bay a ce,

“ ya kai farmaki kan matar sa ne saboda ta saka sunan dan su a matsayin wanda zai ci gadon gidan da ta gina.

“Bayan ya gano cewar ba shine zai ci gadon gidan ba, sai ya watsa ma ta ruwan guba kuma shi ma ya sha ruwan gubar.
“Mutumin yam utu yau, Laraba, da safe yayin da ita kuma matar sa aka garzaya da ita zuwa asibiti. ”

Da ya ke tabbatar da faruwar da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra, Haruna Mohammed, ya ce gawar Okafor na ajiye a dakin ajiye gawa,

“A ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar 2019 ne aka kai rahoto ofishin rundunar ‘yan sanda na 3-3 da ke Onitsha cewar wa wani mai suna Daniel Okafor ya watsa wa matar sa mai suna Paulina ruwan guba.

“Jami’an rundunar ‘yan sanda na ofishin 3-3 sun garzaya zuwa gidan ma’auratan kuma sun yi nasarar garzaya wa da Paulina zuwa Immaculate Heart Hospital domin ceto rayuwar ta.

“Shi kan sa wanda ake zargi da aikata laifin, jami’an mu sun same shi cikin mawuyacin hali kuma sun garzaya da shi zuwa asibitin Multi Care domin a duba lafiyar sa.

“Likitan asibitin ya tabbatar mana da cewar ya sha irin gubar da ya watsa wa matar sa ne .”

Mohammed ya kara da cewa daga baya likita ya tabbatar ma su da cewar Okafor ya mutu yayin da ake kokarin ceton rayuwar sa kuma an ajiye gawar a mutuware domin gudanar da wasu gwaje-gwaje a kan ta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: