TARIHI DA JIHADIN SHEHU USMAN DAN FODIYO
Asalin sa da kabilarsa
Shehu asalinsa Bafulatani ne da aka haifa a Maratta a cikin kasar Gobir a ranar 15 Disamba, 1754 Miladiyya. Sunan mahaifinsa Muhammadu Fodiyo. Asalinsu Fulani ne mutanen Futatoro a cikin kasar Senegal.
A wajen karni na 15 kakanninsa suka yo kaura daga Futatoro suka zo kasar Hausa a zamanin Sarkin Kano Yakubu. Kakansa shi ne Musa Jaffolo, yana daga cikin ayarin da suka zo kasar Hausa. Sun farzama cikin birnin Kwanni wanda ke cikin Jamhuriyar Nijar ta yau.
Yawanci malamai ne masu ba da karatu, sannan kuma suna karantarwa haka kuma suna ɗaukar karatu a inda suka samu malamai. Wani lokaci su kan yi aiki a fadar Sarakai ko su rika koyar da ‘ya’yan Sarakai ilimi. Suna da yawa kuma sun bazu kusan ko’ina a kasar Hausa.
Shehu ya yi karatu a wajen Mahaifinsa da kuma kawunsa, daga nan ya yi karatu a wajen malamai masu yawa a wurare daban-daban.
Daga cikin muhimman malamansa akwai Malam Jibirila na Agadas wanda ake zaton daga gare shi ne Shehu ya samu tasirin yin jihadi,
domin Malam Jibirila ya yi kokarin yin jihadi a kasashen Buzaye. Shehu ya yi yawo da dama, bayan ya dawo gida sai ya kama yin wa’azi da karantarwa a wurare irin su Gobir da Kebbi da Zamfara.
A wannan lokacin ya samu kasar Hausa na yin wasu abubuwa na al’adun gargajiya, kamar su bori da tsafi da haɗa Musulunci da al’adun gargajiya, saboda haka Shehu ya yi tinanin aiwatar da jihadi don ya kawar da al’adun gargajiya daga gurɓata addinin Musulunci.
Haka kuma akwai zalinci mai yawa tsakanin Sarakuna.
Duk irin waɗannan abubuwan ne suka harzika Shehu ya sa ya yi jihadi don a daina cuɗanya Musulunci da al’adun Maguzanci, a daina zalunci da danne wa talakawa ‘yancinsu, a kuma daina nuna bambanci wajen shari’a.
Wannan ya sa ya samu goyon bayan talakawa da dama, domin irin zalincin da Sarakuna suke yi musu.
A lokacin Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo wannan wa’azin na Shehu ya yi tasiri gare shi, don haka ya yi ‘yan gyare-gyare a fadarsa, ya rage haraji ya kuma umarci maza Musulmi suke yin rawani, mata kuma suke yin lilliɓi, kana Shehu ya zama Malamin ‘ya’yansa.
Irin wannan sassauci da Bawa ya yi, Fadawa ba su ji daɗin sa ba, domin an toshe musu waɗansu hanyoyi na samu. Ran ‘yan-bori ya ɓaci ganin an kara wa Musulunci daraja. Bawa ya rasu a 1796 Miladiyya, sai kaninsa Nafata ya gaje shi, da hawansa sai Fadawa da ‘yan-bori suka kara zuga shi,
don haka sai ya soke sassaucin da Bawa ya yi, ya kara haraji aka kuma cigaba da zalinci. Nafata ya ba da umarnin duk wanda bai gaji Musulunci ba,
karda ya shiga wanda ya shiga kuma ya fita.
Nafata bai daɗe ba ya rasu a 1802.
Bayan ya mutu, sai ɗan Bawa wato Yumfa ya gaje shi. An zaci za a samu kyakkyawan sassauci a
wurin Yumfa domin shi ɗalibin Shehu ne, to amma sai abun ma ya kara ta’azzara, zigar Fadawa da ‘yan-bori ta kara karfi. Ya hana mata lilliɓi ya hana maza kuma sanya rawani, sannan ya takurawa duk wanda aka ji yana goyon bayan Shehu Usman Danfodiyo.
A shekarar 1804 , Shehu ya yi hijira daga ‘Dagel ya koma Gudu shi da Almajiransa. A kan hanyarsu Almajiran Shehun suka yi mishi Sarkin Musulmi, kaninsa Abdullahi Fodiyo da ɗansa Muhammadu Bello aka yi musu Sarakunan yaki.
Bayan Shehu ya koma Gudu, sai mutane suka dinga biyo shi, ganin haka sai Sarkin Gobir Yumfa ya yi kokarin hanawa, ya umarci Sarakunansa da kada su bar kowa ya yi kaura zuwa wurin Shehu.
Daga nan suka shiga cika aiki, suka rika kama mutanen Shehu suna azaftar da su, suna kwace musu dukiyoyi amma wannan bai hana mutane zuwa wurin Shehu ba. Da Yumfa ya ga haka, sai ya ɗaura yaki da Shehu a shekarar 1804 , ya samu Shehu a Gudu aka fara yaki
a Tafkin Kwatto inda Shehu ya yi . Aka cigaba da yaki har zuwa shekarar 1808.
Bayan birnin Alk’alawa ya faɗi, sai sauran kasashen Hausa suka mika wuya, inda Shehu Usman Danfodiyo ya dinga ba da izini ko tuta ga Malaman da zasu mulki waɗannan kasashen, waɗanda daga bisani aka koma kiran kasashen tare da Malaman da aka damka wa
tuta da “Tutocin Shehu.” Wato su ne kamar haka:
TUTOCIN SHEHU.
1. Kano- Malam Suleman.
2. Katsina- Malam Umarun Dallaji.
3. Katagum- Malam Ibrahim Zaki.
4. Kazaure- Malam Dantunku.
5. Bauchi- Malam Yakubu.
6. Daura- Malam Isiyaku.
7. Jama'are- muhammadu Wabi
8. Adamawa- Malam Moddibo.
9. Hadeja- Malam Sambo.
10. Misau- Malam Goni Muktar.
11. Gombe- Malam Buba Yero.
12. Ilorin- Malam Abdul’alim.
13. Zazzau- Malam Musa.
An riga an fara bayyanawa a baya kaɗan cewa, Shehu Usman Danfodiyo ya yi jihadi a kasar Hausa baki ɗayanta, inda daga bisani ya kafa daula mai karfi a karkashin cikakken shugabancinsa. An gina wannan daula ne bisa tsari mai inganci da adalci da kyautata ɗabi’u da halayen jama’a.
Shehu Usman Danfodiyo ya rasu a ranar 20 Afrilu, 1817.
IYALAN SHEHU.
Matansa:
■ Maimuna.
■ Aisha.
■ Hauwa’u.
■ Hadiza.
‘Ya’yansa: Daga cikin ‘ya’yan Shehu Usman Danfodiyo guda 23, akwai:
■ Muhammad Bello.
■ Nana Asma’u.
■Abu Bakr Atiku.
■ Sunan Mahaifiyarsa Maimuna.
■ Sunan Mahaifinsa Mallam Muhammadu Fodiyo.
■ Sunan kaninsa Abdullahi Danfodiyo.
KAMMALAWA.
A cikin wannan rubutun, an tsakuro wani abu ne daga cikin rayuwar Shehu Usman Danfodiyo, an tattauna a kansa. Tarihin Shehu Usman
kogi ne mai matukar girma da faɗi.
0 comments: