Dubunwasu masu garkuwa da mutane domin amsan kudin fansa ta cika a Calabar babban birnin jihar Cross River.
Mutane da mace ke masu jagora sun amsa cewa suna garkuwa da mutane, sun kuma ce sun fito daga jihar Delta da Enugu, ne suka canja sheka zuwa Calabar domin ci gaba da satar mutane domin yin garkuwa dasu.
Su dai wadannan mutane da suka ce Calabar yafi dadin aiki sun kwace wa wata mata motar ta ne suka turata waje da ‘yarta da ita wannan mata tayi ihu sai jama’a suka bisu Allah yasa suka cimma su.
Baya da aka kama wadannan mutane jama’a sun nakada masu duka suka kuma yi masu tsirara sa’ilin na aka mika su ga jami’an ‘yan Sanda.
Saturday, 26 November 2016
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: