Saturday, 26 November 2016

Yan Majalisar Majalisar Taraiyya Munyi Martini Akan Maganar Obasanjo

A ranar Larabar da ta Gabata ne tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya caccaki ‘yan majalisun Nijeriya inda ya kira su barayi ya kuma ce ko ‘yan fashi a Nijeriya ba sa sata kamar su. Sannan ya shawarci gwamnatin Buhari da ta taka masu burki.

Toh da alama dai wannan magana ta yi wa ‘yan majalisun daci domin kuwa sun mayarwa da tsohon shugaban martani kuma sun yi wasu tone tone a bisa mulkin sa.

A fadarsu “Idan mu barayi ne masu cin hanci da rashawa, to mu jikokinka ne a bangaren cin hanci da rashawa”. Haka kuma sun zargi tsohon shugaban da yi wa gwamnatin Buhari zagon-kasa.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta hannun mai magana da yawun ta Hon Abdulrazak Namdas, ta bayyana Obasanjo a matsayin “mutumin da ya fi kowa cin hanci a tarihin kasar nan”.

Namdas ya kara da cewa lokacin Obasanjo ne aka baje kudi a majalissar tarayya domin bayar da cin hanci, saboda a sauke Kakakin Majalisar na wancan lokaci Ghali Umar Na Abba.

Obasanjo dai ya kuma caccaki gwamnatin Buhari game da yadda take yi wa gwamnatoci ukun da suka gabata, ciki har da ta sa, kudin goro wajen zargin rashin iya jagoranci.

Ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina korafi kan abun da ya wuce, inda ya ce tun da an zabe shi ne domin ya gyara Nigeria, ya kamata ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya tarar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: