Tuesday, 4 June 2019

Jami’an tsaro sun bazama a garin Kano don tabbatar da tsaro A bikin Sallar yau

Jami’an tsaro sun bazama a garin Kano don tabbatar da tsaro A bikin Sallar yau


Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da cewa ta zuba wadataccen adadin jami’anta a cikin garin Kano domin tabbatar da ganin an gudanar da shagulgulan karamar Sallah cikin lumana, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni a babban ofishin rundunar Yansandan jahar.


A jawabinsa, kaakaki Haruna ya bayyana cewa baya ga jami’an Yansanda da zasu bada tsaro, rundunar ta hada kai da hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, hukumar tsaron farin kaya, NSDC, hukumar kula da dokar hanya ta Kano, KAROTA, da hukumar Hisbah don tabbatar da zirga zirga ababen hawa cikin sauki.
“Mun tanadi tsare tsaren tsaro a filayen sallar Idi, don haka muke kira ga masallata da su guji daukan abinda basu bukata zuwa filin sallar Idi, musamman duk wani abu da zai kawo fargaba ko tsoratarwa ga jama’a.”Inji shi.
Haka zalika kaakakin ya nemi jama’a masu halartar wuraren wasanni da wuraren shakatawa a yayin shagulgulan sallah dasu tabbata sun kasance masu lura da duk wani abu dake wakana a inda suke don kare kansu da dukiyoyinsu daga miyagu.
Daga karshe kaakakin Yansandan yayi kira ga jama’a dasu baiwa hukumomin tsaro hadin kai wajen gudanar da aikinsu, ta yadda zasu samar da ingantaccen yanayi don gudanar bukukuwan sallah cikin nishadi.

Saturday, 1 June 2019

Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade

Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade

Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade


Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasararwa ya yi nade-naden a karo na farko bayan darewarsa kan mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2019.
Sanarwar nadin mukamen na dauke ne cikin sakon da sakataren harkokin mulki na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Ishaq ya fitar a ranar Asabar a garin Lafia.
Ishaq ya ce gwamnan ya amince da nadin manyan masu bawa gwamna shawara na musamman guda tara da za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuni.
Wadanda aka yiwa nadin sun hada da John Mamman, Mai bayar da shawara kan harkokin sarauta; Samuel Egya, Mai bayar da shawara na ofishin gwamna; Yakubu Kwanta, Mai bayar da shawara kan harkokin matasa da kungiyoyi masu zaman kansu; da Murtala Lamus, Mai bayar da shawara kan ayyuka na musamman.
Saura sun hada da Ibrahim Abdullahi, Mai bayar da shawara kan saka hannun jari da tsarin tattalin arziki; James Thomas, Jami'in sadarwa na Abuja; Rakiya Alaku, Mai bayar da shawara kan harkokin mata da bayar da tallafi; Salihu Ogah, Ofishin mataimakin gwamna da Abubakar Zanwa, Mai bayar da shawara kan harkokin shari'a.
Ishaq ya kuma bayyana cewa gwamnan yana son a rika kiransa da Abdullahi A. Sule.

Friday, 31 May 2019

Wednesday, 29 May 2019

Amfanin Na'a-Na'a Ga Lafiyar Dan Adam

Amfanin Na'a-Na'a Ga Lafiyar Dan Adam

Amfanin Na'a-Na'a Ga Lafiyar Dan Adam
Image result for PEPPERMINT plant png
Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or mint] wata shuka ce mai albarka da ake amfani da ita a matsayin maganin gargajiya. Ganyen na'a-na'a kore ne, kamshin ta nada karfi, tana da kamshi mai dadin gaske da filebo mai sanyaya rai. Na'a-na'a nada sinadarin 'minti' 

( wato 'menthol') mai sanyaya rai da lafiyar jikin dan adam. Akanyi amfani da na'a na'a wajen sarrafa wasu kayan amfanin gida da muke siya na yau da kullum, wato kayan amfani da muke siya a kasuwa kamar irinsu makilin (toothpaste), sabullai (soaps), man-shafawa (creams and vaselines), cingam (chewing gum), sinadarin wanke baki (mouthwash) , magungunan shafawa (ointments), da sauransu , saboda kamshinta da amfaninta ga jikin dan adam.

Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a dai ta samune asali ta hanyar auren-shuka , wato auren shuka mai suna 'watermint' da turanci da kuma wata shukar mai suna 'spearmint'. Bincike ya nuna cewa na'a na'a tazo ne daga kasashen turawa da larabawa. Mutanen wadannan kasashen da muka ambata kanyi amfani da ganyen na'a-na'a cikin abinci da kuma wajen shayi, a matsayin ganyen-shayi (tea leaves) haka kuma, akwai man -na'a na'a ( peppermint oil) da ruwanta (peppermint water) a kasuwa domin amfani na daban-daban.

Bincike ya nuna cewa na'a-na'a nada amfani da yawa ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin amfaninta ga jikin mutum sune:
Image result for PEPPERMINT plant png
1. Tana magance matsalar bacin-ciki da rashin fitar bahaya maisa tsugunni
a bayi.
(Ayi shayin na'a-na'a ko azuba manta cikin shayi marar madara.)
2. Tana saukake narkewar abinci
3. Maganin tuka
4. Maganin gudawa
5. Maganin mura da tari [da kuma mura mai damun makoshi - wato 'sore throat']
(ayi amfani da man na'a-na'a ko ganyen , a tafasa ganyen ayi shayi marar madara
, haka kuma, za'a iya amfani da man na'a-na'a cikin ruwan zafi, ayi turiri,
a lullube da mayafi).
6. Maganin ciwon-kai ( a shafa manta wajen da kai ke ciwo).
7. Maganin ciwon-jiki ( a shafa manta ga jijiyoyin jiki dake ciwo
ko wajen dake damunka da ciwo, zata sanyaya, insha Allahu).
8. Maganin ciwon-hakori (ayi amfani da man na'a-na'a da auduga,
a diga man ga auduga , sa'annan a lika ga hakori mai ciwon).
9. Maganin kaikayi
10. Korar sauro ( a shafa man na'a-na'a ga jiki -
hannuwa da kafafu , sauro zai gujesu)
11. Kashe tsutsar ciki
12. Taimakawa hanta wajen aiki
13. Rage yawan damuwa
- tana sanyaya rai da hana damuwa
( a tafasa ganyen
na'a-na'a ayi shayi, ko manta a zuba cikin kofin shayi , safe da yamma).
14. Tana taimakawa kwalwa wajen rike karatu da
kaifin fahimta (ayi shayi da ganyen na'a-na'a a rinka sha da zuma).
15. Tana sanya girki yayi kamshi - filebo ( ayi amfani da ganyen wajen girki).
Hakan zai taimaka wajen son cin abincin (appetite), musamman ga wanda
baya son cin abinci.
16. Tana maganin ciwon-ciki , musamman ga mata masu matsalolin al'ada.
17. Da sauransu.

Monday, 27 May 2019

AMFANIN DABINO A JIKIN DAN ADAM Musamman A watan Ramadan

AMFANIN DABINO A JIKIN DAN ADAM Musamman A watan Ramadan


Dabino na da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun a da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna. Wata malama mai zurfin ilimi a bangaren kayayyakin abinci a Juddah, wato Prof.


 Waddaha Mohammed na cewa, Cin kwayan dabino guda goma mai nauyin 100g zai iya ba mutum wasu abubuwa na amfani ga lafiya jiki. Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium. Ana kimanta zakin sukarin da dabinon ya tattara wajen kashi 78-70 cikin dari na abubuwan da dabinon ya kumsa, kuma wannan sukarin na dabino nan take ya ke narkewa a cikin jini sabanin sauran 'ya'yan bishiya. A nan ne za mu ga hikimar muslunci ta sanya dabino ya zama abin farko da mai azumi zai fara ci,

 wannan don a dawo masa da abubuwan bukatar da ya rasa ne cikin gaggawa, Allah Mai girma ne a dukkan lamarinsa. Ba wannan kadai ba akwai ma 75g na carbohydrate, 63g na sukari, 8g na Dietary fiber, 0.4g na Fat, 2.5g na Protein, 21g na ruwa,0.262 mg na Manganese, 1.32 na minerals. 

 Abin da Prof. Waddaha ta ce shi ne bushasshen dabino ya qumshi: Carbohydrate 79.6%, Fat 2.5%, Water 33%, Minerals 1.32%, Dietary fiber 10%, sai Vitamins A, B1, B2 da C, kamar yadda ya kuma ya kumshi abubuwa da dan dama, a takaice in ka duma dabino shi kadai ya isa ya zama abincin da zai gina jiki in ba don tsoron a yi masa cin koshi ba. Bincike ya nuna cewa dabino ya kumshi sanadaran; Minerals da Calcium, da Protein, da Fat, da Lime, da Coramine, da Dietry fiber, da Phosphor, da da Chlorine, Manganese, da Potassium, da Copper, da Vitamin C, da kuma Magnesium. Da wannan ne za mu gane cewa dabino ya kumshi manya-manyan abubuwa na abinci, wadanda za su gina jiki da jijiya, suma bayyana wa mutum matasantarsa ko da kuwa ya dan kwana biyu, da za a haga dabino da madara tabbas abinci ne mai kyawun gaske, masamman ga wanda yake da matsalar ciki. 

Masana kimiyya na cewa, abubuwan gina jiki da su ke cikin danino na daidai ne da na wani nau'i na nama, ko ribi uku na kifi. Kuma ya kan amfanar da masu cutar fatarar jini, da wasu cututtuka da suka shafi kirji kamar yadda ake kwaba shi a dafa a rika sha daidai gwargwadon yadda aka nunawa mutum. Dabino na amfanar da kananan yara, da matasa, da 'yan wasa, da ma'aikata, da ramammu, da kuma mata masu ciki.

Monday, 25 February 2019

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno


A yayin da a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mai aukuwar ta auku, an gudanar da babban zabe na kujerar shugaba kasa da ta 'yan majalisun tarayya cikin duk wani kwararo, lungu da sako da ke fadin kasar nan.
Bisa ga madogara ta kiyasi da kuma hasashe, tun a yanzu da yawa daga cikin mafi akasarin 'yan takara masu hankoron madafan iko na kujerun mulki a fadin kasar nan, sun fara sanin makomar su ta samun nasara ko kuma akasin haka.
Tun a jiya da yawa daga cikin sakamakon babban zabe na wasu rumfuna da mazabu a fadin kasar nan ya fara bayyana,


Jihar Kano
Karamar hukumar Tudun Wada
APC: 38,865
PDP: 10,707
Karamar hukumar Tsanyawa
APC: 25,823
PDP: 5,399
Karamar hukumar Sumaila
APC: 34,609
PDP: 4,904
Karamar hukumar Gwarzo
APC: 33,581
PDP: 10,638
Karamar hukumar Rano
APC: 23,855
PDP: 7,055
Karamar hukumar Ajingi
APC: 21,458
PDP: 5,267
Karamar hukumar Gezawa
APC: 29,954
PDP: 8,246
Karamar hukumar Bebeji
APC: 26,023
PDP: 8,190
Karamar hukumar Gaya
APC: 25,864
PDP: 6,577
Karamar hukumar Albasu
APC: 19,073
PDP: 6,101
Karamar hukumar Warawa
APC: 19,073
PDP: 6,101
Karamar hukumar Kunci
APC: 20,375
PDP: 4,983
Karamar hukumar Bagwai
APC: 23,375
PDP: 10,584
Karamar hukumar Doguwa
APC:25,454
PDP: 7,031
Karamar hukumar Garko
APC: 22,356
PDP: 2,840
Karamar hukumar Kabo
APC: 29,482
PDP: 8,955
Karamar hukumar Danbatta
APC: 31,850
PDP: 6,947
Karamar hukumar Wudil
APC: 28,755
PDP: 5,108
Karamar hukumar Bichi
APC: 42,714
PDP: 11,050
Karamar hukumar Minjibir
APC: 22,725
PDP: 2,840
Sakamakon zaben kujerar shugaban kasa daga karamar hukumar Gabasawa
APC: 24,420
PDP: 6,130
Karamar hukumar Bagwai
APC: 23,375
PDP: 10,583
A yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya fidda shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya yayin da ya tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kasancewar ta mahaifar sa, Gwamna Ganduje bai yi sake ba wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a karamar hukumar Dawakin Tofa inda shugaban kasa Buhari ya yi nasara da kimanin kuri'u 37,147.
 Buhari ya yi nisan gaske gami da zarra ta fuskar samun nasara akan babban abokin adawar sa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, inda ya samu kuri'u 6,507 kacal a mahaifar gwamna mai ci a jihar Kano.
Sakamakon zaben shugaban kasa daga karamar hukumar Albasu
APC: 26,412
PDP: 10,285
Karamar hukumar Rimin Gado
APC: 17,999
PDP: 12,665
Karamar hukumar Ungogo
APC: 51,842
PDP: 10,475
Karamar hukumar Bunkure
APC: 27,232
PDP: 9,528
Karamar hukumar Tudun Wada
APC: 38,865
PDP: 10,707
Karamar hukumar Tofa
APC: 15,797
PDP: 10,746
Karamar hukumar Kunchi
APC: 21,556
PDP: 4,937
Karamar hukumar Makoda
APC: 24,749
PDP: 3,234
Karamar hukumar Shanono
APC: 24,232
PDP: 8,182
Karamar hukumar Sumaila
PDP: 34,602
APC: 4,904
Karamar hukumar Gwale
Kujerar shugaban Kasa
APC: 50,834
PDP: 12,283
Kujerar Sanata
APC: 40,352
PDP: 21,117
Majalisar Wakilai
APC: 35,276
PDP: 18,997
Kash! Kamar yadda alkalin zaben Mallam Sani Umar ya bayyana a yau Lahadi, Sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya ya gaza fidda kan sa kunya a wurin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Mallam Umar ya zayyana cewa, Atiku ya lashe kuri'u 13,113 yayin da ya sha babban kayi a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takara na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 26, 110 a karamar hukumar Madobi da ta kasance mahaifa ga tsohon gwamna Kano, Kwankwaso.

Dan Majalisar mai wakilcin shiyyar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibrin na jam'iyyar APC ya sha kyar, inda ya sake samun nasara da kimanin kuri'u, 41,071 yayin da abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, ya samu kuri'u 40, 412.
Abdulmunin Jibrin
Sakamakon zabe daga karamar hukumar Garun Mallam
Kujerar shugaban kasa
APC: 23, 810
PDP: 4,861
Kujerar Sanata
APC: 18,412
PDP: 8,548
Majalisar Wakilai
APC: 18,029
PDP: 8,262
Sakamakon zabe daga karamar hukumar Tofa
Kujerar Shugaban kasa
APC: 19,984
PDP: 7,732
Kujerar Sanatan Kano ta Arewa
APC: 16,794
PDP: 10,746
SDP: 397
Kamar yadda Salihu Tanko Yakasai, hadimin gwamnan jihar Kano akan sabuwar hanyar sadarwar zamani ya bayyana s hafin sa na zauren sada zumunta, mun samu cewa, dan takarar kujerar majalisar wakilai na karamar hukumar Madobi, Hon. Kabiru Idris, ya lashe zaben sa.
Honarabul Kabiru na jam'iyyar APC ya lashe zaben sa da kimanin kuri'u 22,100 a matsayin wakilin kananan hukumomin Kura, Garun Mallam da kuma karamar hukumar Madobi da ta kasance mahaifa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LGA
Kujerar shugaban kasa
APC: 88
PDP: 14
Kujerar Sanata
APC: 76
PDP: 28
Majalisar Wakilai
APC: 69
PDP: 28
PU 017, Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LG
Kujerar shugaban kasa
APC:120
PDP: 22
Kujerar Sanata
APC: 8
PDP: 58
Majalisar Wakilai
APC: 78
PDP: 56
PU 019; Jigirya, Kawaji ward, Nasarawa LGA
Kujerar shugaban kasa
APC: 230
PDP: 39
Kujerar Sanata
APC: 165
PDP: 96
Majalisar Wakilai:
APC: 137
PDP: 47
Mazabar Kwankwaso a garin Madobi
PDP: 156
APC: 72
Jihar Adamawa
Dalla-Dalla yadda sakamakon zaben shugaban kasa tsakanin Buhari da Atiku ya kasance cikin kananan hukumomin jihar Adamawa
Karamar hukumar Hong
APC: 20,471
PDP: 23,039
Karamar hukumar Ganye
APC: 20,360
PDP: 17,770
Karamar hukumar Guyuk
APC: 10,825
PDP: 22,059
Karamar hukumar Lamurde
APC: 8,123
PDP: 21,404
Karamar hukumar Yola South
APC: 34,534
PDP: 20,414
Karamar hukumar Mubi South
APC: 19,361
PDP: 10,514
Karamar hukumar Mubi North
APC: 26,746
PDP: 23,156
Karamar hukumar Shelleng
APC: 13,531
PDP: 11,912
Karamar hukumar Girei
APC: 17,765
PDP: 14,673
Karamar hukumar Yola North
APC: 43,865
PDP: 27,789
Karamar hukumar Numan
APC: 10,610
PDP: 23,469
Karamar hukumar Demsa
APC: 6,989
PDP: 29,997
Karamar hukumar Mayo-Belwa
APC: 20,842
PDP: 23,734
Karamar hukumar Madagali
APC: 8,208
PDP: 14,594
Karamar hukumar Maiha
APC: 17,034
PDP: 7,916
Karamar hukumar Song
APC: 17,350
PDP: 22,648
Karamar hukumar Fufore
APC: 29,507
PDP: 16,430
Karamar hukumar Gombi
APC: 12,805
PDP: 18172
Karamar hukumar Jada
APC: 21,332
PDP: 22,877
Karamar hukumar Michika
APC: 10,669
PDP: 32,085
Karamar hukumar Toungo
APC: 7,145
PDP: 5,614
Jimillar sakamakon zaben jihar Adamawa yayin da nasara ta rinjaya zuwa Atiku
APC: 338,927
PDP: 349,690
Karamar hukumar Madagali
APC: 8,208
PDP: 14,594
Karamar hukumar Maiha
APC: 17,034
PDP: 7,916
Karamar hukumar Song
APC: 29,507
PDP: 16,430
Karamar hukumar Gombi
APC: 12,805
PDP: 18,172
Sakamakon Zabe: Buhari ya lashe zaben karamar hukumar Girei a jihar Adamawa
APC: 17,765
PDP: 14,673
Karamar hukumar Mubi ta Kudu
APC: 19,361
PDP: 10,514
Low Cost PU:016; Lokuwa ward, LG: Mubi North
Kujerar Shugaban kasa
PDP: 156
APC: 78
Ajiya ward (Mazabar Atiku)
APC: 186
PDP: 140
PU:10 Unguwar Mbamoi dake fadar Lamidon Adamawa
APC: 228
PDP: 138
Jihar Yobe
Dalla-Dalla yadda ta kasance a kananan hukumomin jihar Yobe tsakanin Buhari da Atiku
1. Bursari APC 22,253 PDP 2,555
2. Jakusko APC 34,424 PDP 3,390
3. Gulani APC 22,858 PDP 2,612
4. Bade APC 42,485 PDP 3,295
5. Nguru APC 36,433 PDP 5,352
6. Yunusari APC 23,837 PDP 939
7. Potiskum APC 62,101 PDP 4,331
8. Fune APC 43,948 PDP 5,707
9. Yusufari APC 22,157 PDP 3,567
10. Fika APC 42,488 PDP , 5522
11. Geidam APC 16,338 PDP 613
12. Tarmuwa APC 12,122 PDP 1,269
13. Damaturu APC 35,772 PDP 2,099
14. Machina APC 14,619 PDP 2,315
15. Karasuwa APC 22,377 PDP 3,692
16. Gujba APC 12,227 PDP 325
17. Nangere APC 31475 PDP 3180
Karamar hukumar Tarmuwa
APC: 12,122
PDP: 1,269
Karamar hukumar Damaturu
APC: 35,772
PDP: 2,099
Karamar hukumar Karasuwa
APC: 22,377
PDP: 3,692
Karamar hukumar Machina
APC: 14,619
PDP: 2,315
Zaben Kujerar shugaban kasa Karamar hukumar Gujba:
APC: 12,227
PDP: 325
PU: Sabon Layi Pri, School; Code: 012 B; LG: Potiskum RA: Bolewa B, Yobe South Senatorial District
Kujerar shugaban kasa
APC: 265
PDP: 12
Kujerar Sanata
APC: 155
PDP: 116
Majalisar Wakilai
APC: 171
PDP: 101
Sabon Layi Pri, School; Code: 012 A; LG: Potiskum RA: Bolewa B, Yobe South Senatorial District
Kujerar shugaban kasa
APC: 248
PDP: 3
Kujerar Sanata
APC: 152
PDP: 98
Majalisar Wakilai
APC: 179
PDP: 57
Jihar Borno
Sakamakon zaben kujerar shugaban kasa na karamar hukumar Mafa
APC: 50,851
PDP: 138
Zaben kujerar shugaban kasa daga karamar hukumar Magumeri
APC: 12,739
PDP: 694
PU 004, Bale Galtimari Jere
APC: 244
PDP: 32
PU 005, Bale Galtimari Jere
APC: 349
PDP: 35
PU 014, Waziri Babagana, Shehuri South Ward
APC: 200
PDP: 7
PU 023 Kukawa, Lamisula Ward
APC: 190https://hausa.legit.ng/1223861-sakamakon-zabe-daga-jihohin-kano-adamawa-yobe-da-borno.html
PDP: 21
Bakin Kasuwa, garin Shaffa, Hawul LGA
APC: 288
PDP: 3
Mandagirau, Biu LGA
APC: 2590
PDP: 154
Ku ci gaba da kasancewa a kan wannan shafi yayin da muka daura damarar kwararo muku yadda sakamakon zaben ke ci gaba da kasancewa a wannan jihohi biyar da muka wassafa.

Tuesday, 19 February 2019

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutum

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta bi Umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, matsawar ya bada odar cewa duk wanda ya fizgi akwatin zabe, to a bindige shi kawai, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar sojin sun yi wannan karin haske ne biyo bayan kakkausan furucin da Buhari ya yi a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu cewa duk wanda ya saci akwatin zabe, to ya yi a ta bakin ran sa.

Wannan kalami na Shugaban kasar a janyo ce-ce-ku-ce , suka da kuma caccaka, duk da dai magoya bayan shugaban na ta kokarin kare dalilan sa na yin furucin.
Dokar zabe dai ta tanadi daurin shekaru biyu ga duk wanda aka kama ya saci akwatin da aka jefa wa kuri’a.

Shi kuma Buhari ya ce a harbe wanda ya saci akwati ya tsere kawai. Ya yi wannan kakkausan kalami ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC jiya Litinin a Abuja.

A na su bangaren, sojojin Najeriya sun kara wa wannan tankiya zafi, yayin da Kakakin su Sagir Musa ya bayyana wa majiyarmu ta Premium imes cewa idan dai shugaban kasa wanda kuma shi ne Babban Kwamandan sojin Najeriya gaba daya, ya bayar da umarni ga sojoji, to babu tantama, ba tababa, kuma babu wani bata lokaci, aiwatarwa kawai za su yi.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa d an takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoplea Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a jiya Litinin, 18 ga watan Fabrairu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna “kalan shi tare da rashin girmama kundin tsari mulki”, ta hanyar furta cewa a bakin ran duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe.


Atiku, a wani jawabin da yayi ta hannun kakinsa, Phrank Shaibu, yace barazana da mutuwa ga mutane a halin shirin gudanar da zabe “kalma ce dake hadda sa rikicin zabe”.

Atiku wanda ya nuna rashin amincewarsa akan shirin tura sojoji a zaben 2019, inda yake bayyana hakan a matsayin rashin dacewa ga damokardiyya, yayi Allah wadai da dabarun tsoratarwa da Gwamnatin Tarayya ke shiryawa.
PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari na harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe – Garba Shehu

A yau, Talata, ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga halin damuwa bayan shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin gudu wa da akwatin kuri’u a zabukan da za a gudanar cikin watan Fabarairu da Maris.

Fadar shugaban kasa ta ce kalaman shugaba Buhari gargadi ne ga ‘yan siyasar da su ka mayar da satar akwatun kuri’u ta hanyar amfani da ‘yan daba al’ada a lokutan zabe.

Da ya ke Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, y aba boyayyen abu ba ne cewar wasu ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin su sace akwatin kuri’u sannan su kashe ma su kada kuri’a ko kuma su raunata su.

Ya ce shugaba Buhari ya yi kalamin ne domin tabbatar da cewar ba a cutar da ma su kada kuri’a ba lokacin zabe tare da bayyana cewar ya kamata a jinjina wa Buhari bisa wannan gargadi ga ma su niyyar sace akwatin kuri’u a lokutan zabe


Kazalika, ya nuna rashin jin dadin sa bisa sukar Buhari a kan furucin da ya yi a kan ma su niyyar sace akwati, tare da nuna mamaki a kan dalilin damuwar su da kalaman na shugaban kasa.

A cewar Shehu, “ mambobin jam’iyyar adawa, musamman jam’iyyar PDP, ne ke sukar Buhari saboda sun gama shirya yadda za su yi magudin zabe ta hanyar satar akwatin kuri’u .

“ Sun fahimci cewar shugaba Buhari ba zai lamunci almundahanar da su ka saba da ita ba wannan karon. Sun nuna abinda su ke niyyar aikata wa, ” a cewar sa.
Shehu ya bayyana cewar duk wanda bashi da wata mummunar manufa a kan zabukan da za a gudanar, kalaman Buhari ba za su dame shi ba.

A cewar sa, “ kalaman Buhari ba za su tayar da hankalin duk mai son a yi zabe sahihi kuma mai tsafta ba. ”

Friday, 15 February 2019

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a  babbar gadarnan ta  Ebonyi

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a babbar gadarnan ta Ebonyi

Babbar magana: An kama wasu mutane biyu yayinda suke shuka bam a  babbar gadarnan ta  Ebonyi


Rahotanni sun kawo cewa an kama wasu mutane biyu a jihar Ebonyi yayinda suke dana bam, a gadar Idembia da ke karamar hukumar Ezza South na jihar.

Gwamna David Umahi ya bayyana hakan a wani jawabi na musamman kan lamarin tsaro ga mutanen jihar a ranar Juma’a, 15 ga watan Fabrairu.

Yace kamun ya biyo bayan rahotannin kwararru cewa wasu mambobi na wata jam’iyyar siyasa na shirin dana bam a kan gadar da wasu wurare a jihar.
Yace wasu mazauna kauyen da ke kusa da gadar wanda ya sada Ezza South da karamar hukumar Ohaozara ne suka kama mutanen biyu.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa dan takarar kiujerar majalisar dokokin kasa na wata jam’iyyar siyasa, yan kwanaki da suka shige ya je wani waje a jihar domin siyan bama-bamai amma masu aiki a wajen suka ki amsa bukatunsa inda suka sanar da gwamnatin jihar

A wani lamari na daban, mun ji cewa kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.
Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe

Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe


Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC za ta dauki hayan jakuna da kekunan hawa domin amfani da su wurin rabar da kayayakin zabe a wuraren da ke ta wahalar zuwa a wasu sassan jihar Gombe.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishinan zabe na jihar, Alhaji Umar Ibrahim a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Gombe a ranar Juma'a.
Ibrahim ya ce wuraren da ke da wahalar zuwa a suna kauyuka ne da ke kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Shingom duk a jihar ta Gombe.

"Za mu dauki hayan jakuna da kekunan hawa da babura domin rabar da kayayakin zabe

"Hakan ya zama dole ne saboda rashin hanyoyin mota shiyasa INEC tayi tanadi da shirye-shiryen yadda za a isar da kayayakin zabe zuwa wuraren," inji shi.

Ibrahim ya ce hukumar tayi tanadi da ya dace a fanin samar da tsaro kuma ta wayar da kan masu kada kuri'a.
Ya kuma ce anyi tanadin takardun kada kuri'a na brail da makafi za suyi amfani dashi kuma kutare suna iya amfani da kafarsu domin dangwala zaben.

Har ila yau, Ibrahim ya kuma ce hukumar zaben tayi tanadin gilashi mai kara girman abubuwa ga wadanda ke fama da ciwon ido saboda su kada kuri'an cikin sauki.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa kwamishinan zaben ya ce hukumar ta tanadi na'urar da za tayi amfani da shi domin ganin yadda zaben ke tafiya tare da kuma samar da mutane masu sanya ido a kan zabe.