Sunday, 20 August 2017

Hotuna: Zahra Buhari da mijinta Ahmed Indimi su na holewa a kasashen ketare

Kuturu da kudin sa, alkaki sai na kasan kwano domin kuwa Zahra Buhari da abin kaunarta kuma mijin ta suna yadda suke so kuma dama ance duk wanda ya samu rana sai yayi shanya

A watannin da suka gabata, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya aurawa wani hamshakin mai kudi na jihar Borno, Ahmed Indimi 'yar sa Zahra Buhari inda aka yi biki na kece raini.

Gagarimin bikin auren na su ya dauki tsawon lokuta ana tattaunawa da tafka muhawarori akai, sanadiyar irin yadda kudi wanda hausawa ke cewa masu gidan rana suka yi ranar a wannan lokaci.

Daga ire-iren kayan aure na tufafi, sha'ani da kuma abinci wanda mutum zai lasa a bakinsa, abin dai ba a cewa komai domin kuwa gani aka ce ya kori ji don kuwa har kwanan gobe kowace yarinya za ta so samun irin wannan daula wajen aurenta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: