Sunday, 20 August 2017

Alamomi 10 na farko da wadanda suka kamu da kanjamau kan fara ji

Daga alamomi da Arewarmu.com dai ta binciko muku a shafin Naij.com ka iya zama mutum na kokarin kamuwa da cutar HIV akwai;

1. Zazzabi da yaki ci yaki cinyewa; idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani, a je ayi tes na cutar kanjamau.

2. Ciwon makoshi, wanda ake kira sore throat, idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya.

3. Kurarraji a fata.

4. Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima

5. Kaluluwa.

6. Yawan ciwon jiki da gabobi.

7. Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba.

8. Barkewar zawo.

9. Yawan ciwon kai, maras dalili

10. Amai ko tashin zuciya.

A kula, ba wai kawai don mutum na daya ko biyu daga cikin wadannan wai lallai yana da cutar ba, a'a. Kawai dai idan sun hadar wa mutum farat ta daya a jika, masana kan ce a je ayi bincike, ko a tari cutar da wuri, idan har ita ce.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: