Wednesday, 16 August 2017

Kiwon Lafiya: Idan Kaji Amfanin Da Abarba Keyi A Jikin Dan Adam Da Kullum Saika Nema Kasha

Binciken masana kiwon lafiya ya bayyana irin fa'idojin da jikin dan Adam zai samu wajen riko da abarba

Abarba ta na daya daga cikin kayana itatuwa na marmari da suke koluwa wajen soyuwa ga mutane sanadiyar dadi da nishadantarwa da take sanya duk wani mai shan ta.

Doriya akan wannan, abarba ta na da amfani masu karfi a jikin dan Adam. Ga kadan daga cikin dalilai da suke sanya kara riko da abarba.

A cikin ko wane kofi daya na ruwan abarba, akwai kaso 100 na sunadarin vitamin C da jikin mutum yake bukatuwa a kowace rana. Kuma wannan sinadarin yana matukar amfani wajen inganta garkuwar cututtuka na jikin mutum.


Sinadarin vitamin C ya na habaka girma da mayar da naman jiki da ya lalace na gaba daya jiki, kuma ya na hana kwayoyin jiki da suke tsufar da mutum da kwayoyin cuututtuka irinsu cutar daji da zuciya.

Bincike ya bayyana cewa karancin sinadarin Vitamin C a cikin hanyoyi da tashoshin jini ya na haifar da kunburin kugu da daskarewar maiko wanda ke janyo nauyin jiki.

Akwai sinadarin Manganese wanda kofi daya na ruwan abarba ya kunshi kaso 75 na wannan sunadarin da jikin mutum ke bukatuwa a kowa ce rana. Wannan sunadarin tare da sunadarin Vitamin C su na haduwa su yi tasiri wajen kawata fata wajen hana yamushewa da tattarewar fata.

Abarba ta na da sunadarin bromelain da yake karya duk wata cuta da ta ke tattare a abinci da ka iya haifar da rashin narkewar abincin, kwarnafi ko tashin zuciya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: