Wednesday, 13 September 2017

Bana karban matsayin da ya sabawa al’adda ko addini na - Rahama Sadau

Fittaciyar jarumar Fim Rahama Sadau ta bayyana cewa ta taba yin watsi da matsayin zama ‘yar madigo don ya sabawa addinin ta. Arewarmu.com

Jarumar ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da jaridar Guardian har tace ta taba yin watsi da matsayin kwaikwayar ‘yan madigo.
'Tatu' sabon fim da rahama ta fito

Ta kara haske a kan matsayin da baza ta iya mantawa tare da yanda ta samu karbuwa a masana’antar Nollywood.

“Na taba samun matsayi na kwaikwayan ‘yan madigo amma sai nayi tunani cewa a gaskiya ‘Rahama’ baza ta iya yin irin wannan fim” cewar jarumar.

Game da matsayin da bata iya mantawa Sadau tace

“ matsayin da aka bani cikin shirin ‘tatu’ wanda na kwaikwayi malaman addinin kirista”

Wani bangaren Rahama da mutane basu taba gani na fito a cikin shirin. na ji dadin matsayin gaskiya.

Duk da cewa babu wani babbanci sosai da yanda nike shiga fitowa kawai na amshi matsayin kuma nayi kamar yanda ake. Arewarmu.com
Game da sauyin zuwa Nollywood Rahama tace tun kafin a dakatar da ita a masana’antar Kannywood take fitowa a fim din Nollywood don ta fito cikin shirin “the light will come” da “ Sons of the caliphate”. Arewarmu.com

“ Babu wani bambanci sosai illa aikin da sabobin fuskoki da kuma sabon yanayi. Labarin da al’adar iri daya ne” inji Rahama.

Tauraruwar fim tace tana da iyaka game da matsayi da take karba kuma baza ta karba wanda yayi sabani da al’ada ko addinin ta.

Jarumar tace tasan Yadda Yan Arewa zasu tunkareta shiyasa take kiyaye wa.

Source: Pulse Nigeria Hausa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: