Wednesday, 20 September 2017

Ya jefa kan sa cikin rijiya: Duniya ta yiwa wani tsoho mai shekaru 70 zafi

Wani tsoho mai shekaru 70 a duniya dake garin Otukpo a jihar Benue, ya bar mazauna unguwarsu ta Okokoro cikin jimami da abin al'ajabi, yayin da ya jefa kan sa cikin wata tsohuwar rijiya.

Shafin Daily Post ta bayar da sunan wannan tsoho a matsayin Inuwa kadai, yayin da aka tsinto gawarsa a wata tsohuwar rijiya dake yankinsu, kuma ya kashe kan sa ne ba tare da barin wata rubutacciyar wasiya ba akan dalilin da ya sanya shi aikata wannan mummuna aiki.

Mazauna wannan yankin sun bayyanawa manema labarai cewa, tun a ranar Juma'ar da ta gabata suka nemi Inuwa suka rasa, domin a tunaninsu ko ya yi batan hanya ne bayan wata fita da yayi.

Gogan naku ashe ya na cikin wata tsohuwar rijiya dake yankin na su, yayin da wayewar garin na ranar Asabar din da ta gabata, mazauna yankin suka ga motsin gawar sa a cikin rijiyar yayin diban ruwa kamar yadda suka saba.

Mallam Inuwa ya mutu ya bar 'ya'ya bakwai, kuma a halin yanzu an sanya gawar a makwancinta a can mahaifarsa ta unguwar Odogomu dake karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: