Monday, 13 August 2018

Katoɓara: Ya kashe kansa bayan Budurwar sa ta ƙi amintuwa da wata buƙatar sa

Mun samu rahoton cewa wani matashi can kasar Zimbabwe, Shupikai Chikuvira dan shekara 29 a duniya, ya kashe kansa bayan da budurwar sa ta hau kujerar na ƙi kan buƙatar sa ta guduwa tare da shi domin cikar burin su na auren juna.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, wasu kauyawa sun yi kacibus da gawar wannan matashi a garin Mutawatawa inda cikin gaggawa suka ankarar da jami'an hukumar 'yan sanda.

Kakakin hukumar 'yan sanda na yankin Gabashin garin Mashonaland, Sufeto Tendai Mwanza, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda jaridar Bulawayo 24 ta kasar ta ruwaito.


Mun fahimci cewa, wannan matashi ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a ranar 4 ga watan Agusta bayan wata sa'insa da ta shiga tsakanin sa da abar kaunar sa.


Sanadiyar sa'insar dai ba ta wuci rashin amincewa da buƙatar sa ta guduwa tare da shi domin su auri junan, inda ta ce hakan ba zai yiwu sakamakon rashin samun albarka daga bangaren iyayen ta.

Rahotanni sun bayyana cewa, Chikuvira dai ya ƙarƙare zancen sa da sahibar sa kan cewa zai kashe kansa, tun da dai ta ƙi amincewa da buƙatar sa da sai gawar sa aka tsinto ta na reto jikin wata itaciya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: