Sunday, 22 October 2017

Tashin Hankali: Uwargida Ta Tura Kanwar Miji Cikin Tukunyar Tafasashen Ruwa Zafi

Jamai’an Hukumar Yaki da Safarar Bil-Adama (NAPTIP) sun cafke wata mata mai shekaru 24, Basira Sagiru, bayan ta tura kanwar mijin ta cikin tafasashen ruwa zafi.

Jami’in da ke kula da harkokin yada labarai tare da hulda da jama’a na hukumar, Josiah Emerole, ya tabbatar wa manema labarai da faruwan hakan a birnin Abuja.


A cewar sa. “Malama Basira Sagiru ta tura kanwar mijin wacce ke zama da su a cikin tafasashen ruwa zafi bayan gardama ya shiga tsakanin su a gidan.


“Wacce aka yiwa rauni, Hasiya Ibrahim, ta ji rauni sosai a yayin ruwan zafin ya kona mata kusan ko ina a jikin kafin mutane su zo su cece daga hannun matan dan uwan. Bayin Allah nan su suka kawo yarinya zuwa hedikwatan mu da ke Abuja.”


Emerole ya ce wacce aka kona a halin yanzu tana hannun hukumar NAPTIP ana mata magani


Ya ce bayan hukumar ta cafke wacce ake zargi, a nan take ta fara gudunar da bincike a kan lamarin; inda ya ce, hukumar za ta san matakin za ta dauka game da lamarin da zaran da ta ida gudunar da binciken ta.

Wannan na daya daga cikin manufofin hukumar na hanna kaskanta dan Adam ta hanyar aiki tare jami’an tsaro don daukaka su, musamman mata da yara.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: