Sunday, 22 October 2017

Waƙa a bakin mai ita: Menene gaskiyar zargin lalata da ake yi a yan matan Kannywood?

Batun lalata da yan matan a Kannywood ya abu ne daya dade ana tattaunawa, inda jama’a ke nuna yatsa ga yan Fim din, yayin da su kuma a nasu bangare suke musantawa.
A wasu lokutta ma ana yi musu zargin akwai yan luwadi da yan Madigo duk a cikinsu, amma a nan BBC Hausa tayi hira da wasu sanannu a harkar ta Fim, wadanda suka yi bayanin yadda lamarin yake.

Rahoton majiyar Arewarmu.com ta bayyana tun bayan fitar wani bidiyo na wata yar Fim yayin da take lalata da wani saurayinta a shekarun baya ne jama’a suka daura ma yan Fim din karan tsana, inda hakan yayi sanadiyyar gwamnatin Kano haramta yin Fim na wani lokaci.


Su ma a Kannywood ana samun zarge zargen Furodusoshi na neman yan mata kafin su saka su cikin fina finansu, amma dai ba’a samu wata da tayi kokarin fitowa ta bayyana hakan ba, in banda wata fitacciyar jaruma daya data bayyana ma majiyar mu hakan.

Ita dai wannan jaruma ta nemi a boye sunanta, ta bayyana ma majiyar ta mu cewa jiga jigan Kannywood da dama sun nemi sun yi lalata da ita kafin su bata Fim, amma ta ki, inda tace Ali Nuhu ne kadai bai taba neman ta ba da niyyar lalata.

Ita ma wata jaruma a fina finan Kannywood, Hauwa Waraka ta shaida cewa duk dayake ba’a taba nemanta da wannan bukata ba, amma gaskiya ba zata kawar da yiwuwar hakan ba, sakamakon kowa da halinsa ya shigo Kannywood.

Shima Ali Nuhu da aka tuntube shi cewa yayi ba shi da masaniya ko kadan da faruwar irin wannan abu, inda yace “A gaskiya ban taba ganin wadda aka ce an yi lalata da ita gabanin a sanya ta a Fim ba, kuma ma har kwamiti muka kafa dake da alhakin lura da hakan.”

Daga karshe majiyar ta tattauna da shahararren Furodusa, Aminu Saira, wanda yace “Wannan batu ba gaskiya bane, don kuwa da ace da gaske ne, da yan matan da suka gabata a Indostri sun koka. Kuma da dama daga cikinsu sun yi aure.”

Sai da wani darakta ya shaida ma majiyar Arewarmu.com cewa sanadiyyar irin badakalar dake cikin Kannywood yasa yake janye jikinsa daga cikinta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: