Tuesday, 21 November 2017

Madalla: Dangote ya bada kyautar makudan miliyoyi domin aikin Allah

Mun samu labari cewa Attajirin Duniya Alhaji Aliko Dangote ya ba wata Kungiya ta Matan Musulmai gudumuwar kudi har Naira Miliyan 100 domin cigaban addinin Musulunci.
Kungiyar nan ta Matan Musulmai watau FOMWAN da ke da hedikwata a Birnin Tarayya Abuja ta samu gina masallaci. Labari ya zo mana daga Jaridar Punch cewa babban Dan kasuwar nan ne watau Dangote da wannan aiki.

Aliko Dangote ya ba Kungiyar gudumuwar kudi har Naira Miliyan 100 ta gidauniyar sa. Shugabar Kungiyar Matan watau Hajiya Amina Omoti ta yabawa kokarin Attajirin inda ta gode masa a bakacin daukacin Kungiyar.

A farkon shekara mai zuwa ake dai sa ran kaddamar da wannan katafaren maallaci a Utako. Kungiyar ta FOMWAN ta nemi wannan taimako ne ta wani babban Jami’in Kamfanin Dangote shi kuma bai yi kasa a gwiwa ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: