A yayin da shekarar 2017 ke kara kawo karshe, babban bankin Najeriya ya kara malalo makudan kudaden da suka kai dalar Amurka miliyan 210 a cikin kasuwar hada-hadar kudaden waje jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na bankin.
Babban daraktan bankin dake kula da harkokin sadarwa da hulda da jama'a Mista Isaac Okorafor dai shine ya sanar da wannan ci gaban ga manema labarai hakan yau Litinin a Abuja.
Arewarmu.com dai ta samu cewa Mista Isaac ya kara da cewa kudaden za'a rabawa dukkan masu mu'amala ne da kudaden kasar wajen da suka hada da gundarin kasuwar da kuma matsakaita da kananan masana'antu.
Haka ma dai mun samu cewa bisa ga wannan dauki da babban bankin ke badawa a kasuwar hada-hadar kudaden, yanzu haka darajar Naira ta kara yin sama inda ake saida dala daya akan Naira 360.

0 comments: