Thursday, 17 August 2017

Shugaba Buhari zai dawo Najeriya don bikin babban Sallah - Inji wata Fitaciyyar jarida

An sanya dawowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa lokacin bikin babban sallah a cewar jaridar Sahara Reporters.
Shugaban kasar na wajen kasar sama da kwanaki 100 don ganin likita a birnin Landan sannan kuma a cewar jaridar yanar gizo, wasu na kusa da shin a shirin dawo da shugabna kasar nan da makonni biyu don bikin babban sallah wato Eif-il-Kabir.

An rahoto cewa uwargidan shugaban kasar, Aisha Buhari ta soke tafiyarta aikin Hajji domin ta kasance a kusa lokacin dawowar shugaban kasar gida Najeriya.

An yi zargin cewa hakan ya saba ma umurnin likitocin dake kula da shugaban kasar yayinda suke son ci gaba da kasancewarsa a chan na wasu makonni hudu.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: