Thursday, 17 August 2017

Rashin Imani: Wasu iyaye sun ɗaure yarinyarsu a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita (Hotuna)

Wasu ma’aurata, Nasiru Adeyemo da matarsa Idayat Adeyemo sun shiga komar jami’an Yansanda bayan da aka kama sud da zargin kokarin salwantar da rayuwar yarsu mai shekaru 7, Abibat Anike Adeyemo.

Yansanda sun Ankara da halin daa wannan yarinya ta shiga ne bayan da jama’a suka gulmata musu bayyanar wani farin buhu akan hanya, wanda yake a daure, inda ba tare da wata wata ba, Yansanda suka dira wajen.

Kaakain rundunar Yansandan jihar ASP Abimbolaa Oyeyemi yace samun labarin ya sanya DPO dake rike da yankin ya jagoranci tawagar yansanda zuwa wajen, idna suka tarar da buhun, kwance shi keda wuya suka tarar da yarinyar a ciki a sume, tare da yatsar ta na hannun dama a guntule.


Daga nan ne yansanda suka garzaya da yarinyar asibiti, inda aka ceto rayuwarta, bayan ta kwashe kwanaki 2 daure a cikin buhun, kamar yadda Arewarmu.com ta ruwaito.

Baya da farfado ne sai yarinyar ta shaida ma yansanda cewa mahaifinta da kishiyar babarta ne suka guntule mata yatsan hannunta, sa’annan suka daure ta a cikin buhun, suka jefar tun ranar juma’a data gabata.

Jin wannan labara ya sanya yansanda baza komarsu wajen neman iyayen wannan yarinya ruwa a jallo, inda suka samu nasarar kama su a ranar Lahadi 13 ga watan Agusta. Kuma tuni an fara bincike akansu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: