Wednesday, 11 October 2017

Dan baiwa: Labarin wani hazikin Makaho da ya kammala karatu a Jami’ar ABU Zaria

Mun samu labari cewa wani makaho ya kammala Digiri a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da maki mai tsoka a yanzu haka.

Ga wani Bawan Allah dan baiwa mai Usman wanda makaho ne kuma zakakuri a ajin sa. Usman ya kammala karatun sa na Digiri yanzu haka a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fannin aikin jarida da kafofin yada labarai.


Wani Malamin sa mai suna Muhammad Hashim Suleiman ya bayyana cewa Usman yana cikin hazikan da ke ajin sa asali ma ya kammala karatun na sa ne da mataki mai tsoka. Usman dai ya san muryar kowane Malamin sa ko da ba ya iya ganin su.

Usman yana aiki ne da wata na’ura ta makafi wajen karatu Inji Malamin sa. Usman kuma Musulmi ne mai kishin addinin sa kuma babban Aminin sa wani Kirista ne mai suna Silas tun farkon shigowar sa Jami’a kuma yanzu haka yana soyayya da wata yarinya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: