Labarin Bawa Dorugu: Bahaushen Farko Da Ya Fara Zagaya Turai
Gabatarwa
Wannan labari, Dakta J. F Schon ne ya karbe shi daga bakin shi kansa Dorugun a shekarar 1883, a ka wallafa shi a kasidun kasar Ingila a wuraren shekarar 1885. An kuma karbi labarin ne ta hanyar Dorugu, inda ya ke bayar da labarin a cikin harshen Hausa, Dakta Schon kuma ya na rubutawa da harshen Turanci.
Dorugu dai bawa ne, Bahaushe mai yin bincike a kan sassan Afirka ta yamma, wanda Dakta Barth ya siya a kan hanyarsa ta komawa Kasarsa ta Germany, bayan zuwan sa Kasar Hausa, ya kuma isa da shi Kasar Ingila da Germany a wajajen shekarar 1856.
Haka zalika, a wuraren shekarar 1906, an ce Turawan mulkin mallaka sun dauki Dorugu aikin koyarwa, inda ya rika koyar da dalibai a garin Zangeru da ke Arewacin Nijeriya. Don haka wannan labari somin tabi ne kafin mu kawo muku tarihin zuwan Dakta Barth da wani abokinsa mai suna Adolf Oberweg Kasar Hausa, tun a wajajen shekara ta 1850. Asha karatu lafiya.
Kuruciyar Dorugu
Dorugu ya fara da cewa “ Sunan garin da aka haife ni Dambanas, kusa birnin Kanje, tafiyar yini guda ce kacal a tsakani daga Dambanas. Mahaifina ya kasance tare da mahaifiyata, sunansa Kwage. Amma Adam ne asalin sunansa; mhaifiyata kuma sunanta Kande. Haka nan, ina da kanne guda biyu, daya namiji dayar kuma mace. Namijin sunansa Bakurau, macen kuma Simanta wadda aka fi kira da Ta-roko.
Baki dayanmu, an haife mu a gari guda. Mahaifin namu ya zauna a wannan gari har tsawon shekaru da dama yana kida da dundufansa; yana kuma yin aiki a wata gonarsa karama, amma mu saboda karancin shekaru, ba ma iya taya shi aikin yadda ya kamata. Da na ga mahaifan nawa suna shan wahala a gona, sai na cewa, mahaifina zan fara taya shi aikin gonar, ya ce da ni, ba ka isa fara yin aiki ka’in da na’in ba, ka jira zuwa shekara mai zuwa, na ba ka baiwa daga nan sai ka fara yin aiki.
Daga nan ne kawai na fara yin kuka, don dokin ganin na fara aikin. Bayan mun koma gida ne, ya fadi a gaban wani Makeri (mai sana’ar kira), ya nemi da ya kera min baiwa. Haka kuwa aka yi, bayan mahaifina ya kawo min, na yi ta faman murna.
Da gari ya waye muka tashi, muka tafi gona da sassafe. Mahaifiyata kuma ta yi zamanta a gida ta yi mana tuwo; da nufin idan ta kare ta kawo mana gona. A duk lokacin da suka tsaya cin nasu tuwon, ni ba na so na tsaya na ci nawa, saboda jin dadin aikin noman da nake yi.
Kazalika, mahaifin nawa kan tafi ya kirawoni, har yakan ce da ni kaci naka tuwon mu ci namu, kana sai in tafi na ci nawa tuwon. Da mu ka ga ba mu samu amfanin gona mai yawa a wannan shekarar a gonar ba, sai mahaifina ya bar wannan gonar ya koma wata a kusa da gidan namu. Da muka noma wannan ta kusa da gidan namu, mun samu hatsi ko amfanin gona, amma ba mai yawa ba. Baya ga wannan gonar, muna da wata ta noman auduga wadda ita ma muke noma a cikin ta, ni da mahaifina, kanwata kuma a daidai wannan lokacin, ba ta ji dadi ba, ma’ana ba ta da lafiya.
Wata rana, mahaifiyarmu ta tafi da mu gonar auduga, da yamma ta yi muna kan hanyar dawowa gida, sai na hangi kanina daga kan wani tudu, yana daga cikin gida tare da wani karamin yaro. Sai mahaifiyata ta ce da mahaifina, wannan ba Bakurau ne da Taroko ba? Muka yi mamaki muka ce, lallai ta samu lafiya shi yasa har ta fito waje ta ke yin wasanta.
Da muka isa cikin gidan, sai na ga ashe ba kanwar taw aba ce, wani yaro ne da ban. Daga nan na yi gudu na shiga cikin daki na kira sunanta, na ce Taroko, Taroko, amma ina! ban ji motsinta ko amsar ta ba. Nan ne na tabbatar da cewa, ba ta yin motsi. Ga wajen da ta kwanta duk ta dalale shi da yawu, da na sake dubawa, a nan ne na tabbatar da cewa, ta mutu; na yi kuka sosai.
Da mahaifina ya ga haka ya dauke ta, nan da nan sai ga hawaye na ta kwaranya a kasa daga idanuwansa. Haka nan mahaifita, ita ta fashe da kuka, kanina kuwa, shi bai ma san abin da ake ciki ba, saboda rashin wayo.
Daga nan ne mahaifin namu ya tambayi kanin nawa cewa, ka ba ta fura? Ya ce, eh, ka ba ta ruwa? ya sake cewa, eh. Daga sai ya yi shiru bai sake cewa komai ba. Can bayan jimawa, sai ya ce, tunda ba ta mutu da yunwa ko kishirwa ba, babu laifi. Ya kira wani abokinsa ya ce da shi, ya gina masa kushewa da za a binne ta a ciki. Haka ya dauke ta ya kai ta, ya sata a cikin kushewa ya dora ita ce a bakin kushewar ya rufe ta, kana ya mai da ya rufe ta da kyau.
Bayan gari ya waye, mahaifina ya tambayi mahaifita cewa, me za mu saya mu yi ma ta sadaka da shi? Ta ce da shi, mu sayi wake a dafa a kai gaban manyan mutane ya ce, haka yay i daidai.
Ya tafi ya sayo wake ya kawo mata. Ta dauko hatsi ta yi fura ta kuma dafa waken muka dauka muka kawo gaban manyan mutane a dandali. Da suka ci waken su ka sha fura suka kare, sai Malamai suka yi alfatiya, muka tafi muka zauna.
Lokacin Yaki
Bayan mutuwar kanwata, sai na ji labarin cewa yaki na nan zuwa garinmu. Mu ka tashi da dare muka gudu, inda muka yi tafiyar kwana biyu ko uku a kan hanya. Ashe, labarin ba gaskiya ba ne. Da gari ya waye mutane suna ganin ‘ya’yansu sun gaji da tafiya, ni da kaina haka na rika yin kuka saboda gajiya.
Da zarar an ji jariri na yin kuka, sai a ce da mahaifiyarsa, ki ba shi nono ya sha don ya yi shiru. Da mu ka zauna a cikin dokar daji, ina tsammanin wadansu mutane sun dawo cikin gari sai suka ga garin namu babu mutane kowa ya gudu, daga nan ne suka dawo suka fada mana. Akwai wani barawo da ya zauna a cikin garin ya rika sace abubuwa da dama, wanda har sai da muka dawo muka sake samun sa a garin. Bayan mun dawo ne muka samu an kona baki dayan garin, ashe wannan barawon ne ya sanya wa garin wuta. Gidanmu ne kadai da na wata tsohuwa suka rage wutar ba ta kone su ba.
Da muka yi sa’a muka samu gidanmu babu abinda ya taba shi, sai muka shiga mu ka zauna, ma ta su ka shiga neman tukwanensu na girki, amma ba su samu ba har sai da suka zagaya gidan wannan barawo suka samu tukwanensu a daure a can suka dauko kayansu.
Mafarin jin labarin yaki kenan.
“Da muka zauna kamar shekara daya, sai muka kara jin labarin yaki daga wani gari izuwa gare mu. Sai muka gudu muka tafi daji, amma ba nesa daga garinmu ba. Muka kwana a daji, da Safiya ta yi muka ga wasu mutane ‘yan kabilar Fulani a kan dokuna daga nesa, muka hau saman bishiya muna leken su.
Muna gani wasu mutane suka saka wa wani gari da ke makwabtaka da namu wuta, sai hayaki kawai ke tashi, sannan suka yi tafiyarsu. Sai can wani yaro ya ce ya hango wasu mutane na zuwa inda muke da gudu, domin sun hango shi suna kan bishiya. Fadin haka ke da wuya, mahaifina da wadansu mutane suka tafi don tarbo su. Da suka gamu da su a cikin lukuki, sai suka ce da su “namu ko ba namu ba?”
Mutanen nan kuwa su biyu ne, sai suka amsa da cewa “naku”. Shi kenan sai suka dungumo suka dawo inda mu ke. Dukkanin mu sai muka dau murna, don mun san su. Muka tambaye su “yaya kuka san muna nan” sai suka ce, ai sun hango dayanmu ne a kan bishiya.
Muka tambaye su labarin cikin gari, suka ce mana wadansu an kashe su, an kuma ji wa wasu raunika, wadansu kuwa an kame su a matsayin bayi. Muna kallo wasu suka rika dibar dukiyarsu suna komawa garuruwansu.
Sunan garin da fulani suka yi fada da shi, Shagari. Bayan sun ba mu wannan labari, sai muka dawo muka zauna a garinmu tunda yakin bai karaso mana ba. Ba a dade ba kuma, sai muka kara jin labarin wani yakin, aka ce wai Sarkin Borno Shehu Umar, yana nan zuwa don yin fada da wani gari mai suna kanche.
Da ya tafi ba a gane shi ba, sai da rana ta yi aka ga kurarsa, aka samu ya yi fada da Sarkin kanube ya ba su kashi ko ya buge su, ya sa wuta a garinsu ya dawo garinsa. Ya kuma kwashi dukiyarsu mai yawa, suna tafe suna buga bindiga, har ma muna jiyo karar daga garinmu Dambanas. Haka ma da suka isa wani gari mai suna Tasau, sai da suka yi fada da shi.
Mutanen Tasau sun iya yin fada kamar wuta, kuma ba a ci su da yaki ba, sai Sarkin Borno ya wuce garinsa, ashe akwai dakarunsa da ba su tafi ba. A wannan lokacin, akwai yunwa, don haka sai mahaifin mahaifiyata ya zo ya dauke mahaifiyar tawa. Ya ce da mahaifina “ba ni labarin diyata ta gidanka, ka da ta mutu da yunwa”.
Mu na kuka da ni da kanina, ya dauke ta zuwa wani gari mai suna Bangasa, inda ya aurar da ita ga wani mutum, duk da cewa, ba ta sonsa. Takan gudu ta dawo gidan ubana, mahaifinta ya zaga ya sake mayar da ita.
Mu hadu a mako na gaba da yardarm Allah.
0 comments: