Thursday, 16 February 2017

Takardun lamunin Najeriya sun yi kasuwa a Turai

Kasuwar sayar da hannayen jari a London ta fitar da takardun lamuni na gwamnatin Najeriya na Dala bilyan daya.

Takardun bashi da za su bai wa Najeriya samun wadannan kudaden bashi daga hannun wadanda suka saya ita kuma ta dinga ba su kudin ruwa na tsawon shekaru goma sha biyar kafin ta biya.

Alhaji Kasimu Garba Kurfi, jagoran kamfanin hannun jari a Najeriya, na Apt Securities ya yi mana karin bayani a kan dalilin da yasa Najeriya ta nemi lamunin na dogon zangron da ya fi kowane tsawo.

Ya kara da cewa gwamantin Najeriya ta yi wa hannayen jarin London din bayani dalla-dalla a kan abubuwan da za ta yi da kudin.

Najeriya ba zata karbo kudaden ba ne domin ta kashe su sai dai don a yi hanyoyin jiragen kasa da su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: