Likita wane ciwo ne ake kira progeria a likitance? Ina so a yi mini bayaninsa. Shin yana da magani?
Amsa: To, a binciken da na yi maka game da wannan ciwo, wanda yana daya daga cikin cututtukan da ke sa a ga yara da siffar tsofaffi, an rawaito cewa ciwon gadonsa ake yi, sai dai da yake masu ciwon ba su cika wuce shekara 20 zuwa 30 a duniya ba, ba su cika yin auren da ma za a samu ’ya’ya masu irin matsalar tasu ba. Wannan kan takaita yawan masu cutar.
Ba a cika ganinsa a irin kasashenmu ba, an fi ganinsa a can kasashen Turai da Asiya. A can din ma ba su wuce yara 100 a halin yanzu ke raye da wannan ciwo ba. An dai taba ganin guda daya a Afirka.
Alamun ciwon su ne da zarar yaro ya fara wuce shekara biyu sai a ga ya fara lalacewa cututtukan da ke sa a ga yara da siffar tsofaffi, an rawaito cewa ciwon gadonsa ake yi, sai dai da yake masu ciwon ba su cika wuce shekara 20 zuwa 30 a duniya ba, ba su cika yin auren da ma za a samu ’ya’ya masu irin matsalar tasu ba. yana kanjamewa, fatarsa na tattarewa, sumarsa na zubewa, gani na yin rauni, hakora na zubewa, amma karfin jiki da na tunani na nan garau.
Wadansu da dama nan da nan suke cikawa, wadansu sukan girma da wannan sifa ta tsofaffin mutane.
Babu magani na warkewa, yawanci sai dai ’yan magunguna masu rage musu wahalhalun da ke tattare da ciwon akan ba su kafin lokaci ya yi.
Wannan ciwo na daya daga cikin cututtukan da masana kwayoyin halittun jikin dan Adam suka tsananta bincike a kansa, domin gano ko akwai magani; abin da ke sa su hakan shi ne suna ganin cewa gano maganin wannan ciwo wai zai iya silar gano maganin tsufa!
Yaro ne shekarunsa 22 amma kansa ya fara furfura kuma abin ya dame shi. To me yake kawo haka kuma ko akwai yadda zai ya rabu da ita?
Daga Usman Ali Yakasai
Amsa: A’a, wannan ai ba abin damuwa ba ne, ka nuna masa bayanin ciwon da aka yi a sama, ya san ai shi baiwa ce ma aka ba shi, kamar yadda wadansu masu iya magana kan ce: furfura ga yara baiwa ce. Idan abin dai ya ci gaba da damunsa za ka iya gaya masa akwai zabin tura kan (dyeing). Idan ya je wurin masu askin baba na zamani za su taimaka.

0 comments: