Sunday, 5 March 2017

Yadda za’a tsige Buhari daidai da kundin tsarin mulki – Sanata Ibrahim

Sanatan Najeriya, Ibrahim Tsauri yace shugaban kasa Buhari na iya dadewa yadda yake so a wajen kasar idan har ya mika mulki ga mataimakin sa don yayi aiki a matsayin mukaddashi.
Sanata Ibrahim Tsauri wadda ya kasance jigon jam’iyyar Peoples Demo cratic Party (PDP) ya bada sharadin da zai iya sawa a iya tsige shugaban kasa.

Sanatan wadda ke wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya tsakanin 2003 da 2017 yace za’a iya tsige shugabna kasa idan aka tabbatar da gazawar sa, a cewar jaridar The Sun.

Ya bayyana cewa: “Kundin tsarin mulki ya bayyana cewa idan aka tabbatar da gazawar shugaban kasa, za’a iya tsige shi ko da ya yanke shawarar barin aiki ko kuma bai yanke ba.”

A cewar sa, shugaban kasar na iya tsayawa hutu har na dogon lokacin da yake so idan har ya mika mulki ga mataimakin sa.

“Kundin tsrin mulki na nan kuma ya tabbatar da haka. Idan shugaban kasar ya bar kasar don wani abu, sannan ya mika mulki ga mataimakin sa kuma Buhari ya aikata haka kuma ya cike dukka ka’idojin.

“Shugaban kasar ya bar kasa don duba lafiyarsa sannan yayi abunda kundin tsarin mulki ta bukaci da yayi. Bai kamata mu dami kanmu game da dadewarsa shugaban kasa a wajen kasar ba tunda ya mika mulki ga mataimakin sa.

“Wannan dalilin ne yasa ma baku kira shi mataimakin shugaban kasa ba a yanzu, kuna kiran shi da mukaddashin shugaban kasa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: