Sunday, 5 March 2017

Su waye za su yi takara da Buhari a zabe mai zuwa?

Jaridar Daily Trust tayi wani nazari inda ta kawo jerin ‘yan siyasan da ke shirin tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019 a Jam’iyyar APC mai mulki da kuma Jam’iyyun adawar kasa.

Muhammadu Buhari

Duk da dai yanzu shugaba Muhammadu Buhari ba ya kasar kuma bai taba nuna cewa zai tsaya ko ba zai tsaya takara a zabe mai zuwa ba. Na kusa da shi dai abin da suke nunawa shi ne shugaban kasar zai yi tazarce har shekarar 2023. Idan har hakan ya faru shugaba Buhari zai ajiye mulki yana shekaru fiye da 80 kenan.


Yemi Osinbajo

Mataimakin Buhari kuma Mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo na iya tsayawa takara a zabe mai zuwa musamman idan har shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba. Farfesa Osinbajo ya samu shiga wajen Buhari ba shakka, sai dai anya APC za ta yarda Osinbajo ya rike mata tuta?


Bola Tinubu

Daya daga cikin manyan jiga-jigan APC Bola Ahmed Tinubu na iya tsayawa takara a zabe mai zuwa. Ko da ma can ya nemi ya tsaya tare da Muhammadu Buhari a zaben baya. Bola Tinubu dai ya fito kwanan nan yace ba zai taba adawa da Buhari ba. Idan har Buhari ba zai tsaya ba…

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: