Amsa: Wannan tambaya taka tana da muhimmanci sosai, domin akwai mutane da dama da ba su san amfanin gashin cikin hanci da na kunne ba.
Gashin cikin hanci da na kunne suna daga cikin sassan jiki masu taimakawa wajen yakar kwayoyin cuta. Hikimarsu ita ce duk kwayar cutar da za ta shiga hancin ko kunnen su riketa kada ta shige, kai kuma idan ka tashi wanka sai ka sa hannu ka dan wankosu waje, ka ga an hana wasu kwayoyin cuta shiga jiki ke nan.
Yawan irin wannan gashi yakan bambanta daga wani zuwa wani. A wasu dan kadan ne, sai an kura ida sosai za a gani, a wasu kuma har lekowa waje suke. A wasu kuma akwai tsaka-tsaki. To masu shi da yawa din, wadanda yakan yi yawa har ya leko waje ba kyan gani, sune ake so su dan rika rageshi, ba askeshi tatas ba.
Sa’annan har ila yau, a can cikin hancin da kunnen, da ma hanyoyin numfashi akwai wasu nau’i na kananan gashi wadanda ido ba ya gani masu tare kwayoyin cuta, idan an yi tari ko atishawa a feso su waje.
0 comments: