Thursday, 13 July 2017

Wasu Abokai 4 Sun Yiwa Wata Daliba Fyade (Hoto)

Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Osun sun bayyana cewa sun kama wasu dallibai gudu 4 ‘yan makarantan kwalajin koyarwa na Adeyemi College of Education (ACE) a jihar Onda wadanda suka yiwa wata yarinya fyade.

An gabatar da wadanda ake zargi da suna Olakunle Adetuyi, Timilehin Akinola, Tobi Olagbaju and Adebisi Adeyemi, wadanda shekarun su bai wuce 24 zuwa 26 ba. Har yanzu jami’an tsaro na neman dan uwan su guda wanda aka suka aikata laifin tare da shi mai suna Eric Nwage.
Ita wadda aka yiwa fyaden daliban Tarihi da Turanci ne ‘yar shekara 22 sannan kuma budurwan daya daga cikin wadanda suka aikata laifin ne Timilehin Akinola
A lokacin da ake gabatar da masu laifin ga manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda na jihar a birnin Akure, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ondo, Hilda Ibifuro-Harrison, ta bayyana cewa wadanda ake zargin su yaudare yarin ne zuwa gidan Olagbaju dalibin makaranta Rufus Giwa Polytechnic Owo ne sannan kuma abokin Timilehin.
A yayin da dalibar ta isa gidan Olagbaju gida mai lamba 17 a Funbi Fagun Housing Estate a birnin Ondo, a nan ne suka samu nasaran yi mata fyaden.
Daya daga cikin abokiyan wadda aka yi ma fyaden ne ta kai kara wurin jami’an tsaro masu zaman kan su, wadanda su suka kama wadanda suka aikata laifin bayan sun gudunar da binciken suka mika su hannun ‘yan sanda domin a hukunta su kamar yadda doka ta tsara.
“Daya daga cikin wadanda ake zargi, Olakunlle ya dauke bidiyon su a yayin da suke aikata wannan mummunan aikin’
inda a ciki bidiyon suka fada mata cewa za su mata asiri idan har ta kai su kara”
“A lokacin da ‘yan sanda ke gudunar da binciken su, sun gano wayar da layar da suke gaya mata cewa za su mata
asiri da shi”
Kwamishan ta kuma kara da cewa, yarin wadda aka wa fyaden na asibiti ana mata magani a asibitin Ile Ife, a jihar Osun.
A lokacin da ya ke furta wa bayan ya amince da aikata wannan laifin Mr. Akinola ya bayyana cewa shi da abokan sa sun yiwa yarin fyade.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: