Rahotanni daga kafafen yada labarai na Rediyo Jigawa na cewa gwamnatin jihar Jigawa zata tallafawa matasa kimanin 10,000 a kan noman rani domin su kasance masu dogaro da kansu.
Alhaji Hamza Muhammad Hadejia, mataimaki na musamman ga kan shigar da alumma cikin harkokin gwamnati, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummomin garuruwan Tsagewa, da Jamaga, da Yalo, da kuma Darmomuwa wadanda da su ke karkashin kananan hukumoin Miga da kuma Kaugama.
Alh. Hamza Muhammad Hadejia,
Mataimaki Gwamnan Jigawa Na Musamman
Ga Kan Shigar Da Al-Umma Cikin Harkokin
Gwamnati.
Mataimaki Gwamnan Jigawa Na Musamman
Ga Kan Shigar Da Al-Umma Cikin Harkokin
Gwamnati.
Alhaji Hamza yace, gwamnatin jihar Jigawa ta bujuro da kyawawan manufofi da tsare-tsare domin cigaban alumma ta hanyar farfado da aikin gona da sabbin dabaru noma irin na zamani.
Matasa daga yankunan Yalo, da Darmomuwa, da Jammaga, da kuma Tsagewa za su gajiyar shirin noma a filin noma na Tsagaiwa mai fadin kadada dubu daya da sabain da hudu domin bunkasa tattalin arzikinsu.
0 comments: