Saturday, 11 March 2017

Yanda Zakai Amfani Da WhatsApp A Computer Cikin Sauki

Wata sa’a rubuta sakonni ko kuma tattaunawa da mutane a wayar hannu na android abu ne da kowa ya sani mai yiwuwa, amma a kowani lokaci rubutu a kan naurar kwamfuta yafi sauki.

Domin haka ya sanya Kamfanin WhatsApp ta fitar da hanyoyi 2 daban-daban da mutum zai iya amfani da sabis din na su a ta kwamfutarsa: wato WhatsApp ta yanar gizo a kwamfurta Windows da OS X.
Abubuwan Da Mutum Ke Bukata Wajen Hada WhatsApp A Kwamfutarsa
A cewar shafin kamfanin WhatsApp ta yanar gizo, mutum zai iya amfani da sabis din WhatsApp (ta yanaz gizo ko a kan kwamfuta ta App) idan har wayar hannun sa na daya daga cikin wadan nan:
• Wayar Android
• Wayar iPhone 8.1+
• Wayar Windows Phone 8.0 and 8.1
• Wayar Nokia S60, Nokia S40 EVO
• Wayar BlackBerry and BlackBerry 10
Idan har mutum zai yi amfani da WhatsApp a Kwamfutarsa, wayar hannun say a kasance tare da data ko Wi-Fi wajen hadawa. Saboda dandalin na aiki tare sabis din WhatsApp da ke wayar hannu mutum wajen gudunar da aikin.
– Misali, idan mutum zai yi tafiya zuwa wani kasa sannan sabis din waya da ke garin wayar hannun sa, mutum ba zai iya amfani da sabis din WhatsApp a wata waya da ba na sa ba.
Yadda Mutum Zai Saita WhatsApp Ta Yanar Gizo
A farko, zaka saita wayar ka da sabis din WhatsApp ta yanar gizo;
1. Mutun na da daman yin hakan ta kwamfutar ta daya daga cikin wadanda nan hanyoyin daban daban na neman abu ta yanar gizo na Google chrome, Opera, Safari ko Edge, ko kai tsaye mutum tafi zuwa https://web.whatsapp.com
2. Daga nan mutum zai ga hadaddiyar lamba (QR Code) wacce zai tanzance ta hanyar amfani da manhajar WhatsApp da ke kan wayar sa. A karkashin lambar, za a samu bayani dalla dalla game da yadda za a yi hakan. Misali a wayoyin IPhone, idan mutum ya latsa alamar saiti (Settings) zai ga inda aka rubuta ‘WhatsApp Web
3. Bayan mutum ya dauke hoton lambar, daga nan zai iya ganin sakonnin sa da ke kan WhatsApp na shi a wayarsa sannan kuma a Kwamfutarsa.
Sabis din WhatsApp ta kwamfuta shigen daya ne da na waya, sai kawai banbanci kawai shi ne a babban naurar kwamfuta ce. Mutum zai iya amfani da duk wani sabis da ya kan yi amfani da shi a WhatsApp wayarsa ta kwamfuta.

Yadda Mutum Zai Saita App Ta WhatsApp A Kan Kwamfutarsa
Saita app na WhatsApp a kan kwamfuta daya ne da yadda a ke saiti WhatsApp ta yanar gizo, sai dai banbancin kadan ne, – – – mutum sai ya yi downloading sannan kuma sa app din a kan kwamfutarsa.
1. Mutum a farko zai yi downloading app din app sabis din WhatsApp kwamfutarsa na Mac ko Windows daga whatsapp.com/download ta kwamfutarsa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: