Thursday, 16 March 2017

Yanda Wani Jami'in Gwamnati Ya Ajiye Aiki A Jahar Bauchi

Maitaimakawa gwamnan jihar Bauchi akan harkar kasuwanci da saka jari, Samaila Sanusi ya ajiye aikinsa a dalilin rashin jindadin aikin da ya keyi.

Hakan shine karo na biyu da wani jami’I a gwamnatin Mohammed Abubakar na jihar Bauchi ke ajiye aikinsa saboda rashin jin dadin yanayin aikin.

Bayan haka kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Tafawa Balewa Munnir Yisin shima ya ajiye aikinsa.

Samaila Sanusi yace ya dade ya na neman wannan damar domin ya ajiye aikin nasa amma hakan bai yiwu ba saboda yana ganin ko matsalolin da yake fuskanta a jihar zai warware amma jiya iyau.

“ Nayi iya kokarin ganin mun tattauna da gwamnatin akan matsalolin da muke fuskanta musamman a mazabun mu amma hakan ya ci tura.”

A watan Disembar bara ne kwamishinan kasafin kudin jihar Shehu Ningi ya ajiye aikinsa bayan kin amincewa da yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da ayyukanta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: