Friday, 17 March 2017

Abubuwa na neman ya kwace ma Buhari, dole ya mike tsaye – Inji El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari wadansu daga cikin na kusa dashi kamar sakataren gwamnatin tarayya, David Babachir da Abba Kyari suna yin yadda suka da ma a gwamnatin.

El-Rufai ya fadi hakanne a wata takarda da ya rubuta wa shugaban kasa domin gaya masa yadda ya kamata ya mulki kasa Najeriya sannan kuma da sanr da shi yadda ya bari abubuwa ke ta tabarbarewa a kasa Najeriya.

Y ace Buhari ya yi watsi da irin manufofin da suka yarda akai a lokacin da aka kafa jam’iyyar sannan kuma nuna rashin ko in kula da neman shawara daga gwamnonin jam’iyyar masu ci da wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a wancan lokacin.

El-Rufai y ace ita kanta jam’iyyar APC din a waste take saboda Buhari ya kasa rike ta a matsayinsa na shugaban kasa.

“ Hakan zai iya zama ba rishin ka bane amma mutane daga nesa haka za su gani”

“ Wadannan ‘yan siyasar kansu kawai suka sani amma bawai jam’iyyar ko kuma ‘ya’yan jam’iyyarba”

“ Sakataren gwamnatin tarayya bai san komai ba akan siyasa sanna kuma bay a ganin kowa da gashi a ido. Yana taka duk wanda yaso a jam’iyyar, gwamnane kai ko jigo a jam’iyyar APC din.

“ Ana ta yada zantuttuka a jaridu cewa wai ba ka da iko a gwamnatinka sannan sai yadda wasu suka yi da kai a gwamnati

El-Rufai yaba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari akan yadda zai gyara kasa Najeriya musamman fannin Ilimi, sufuri da kiwon lafiya.

El-Rufai y ace dole ne Buhari ya sanarwa ‘yan Najeriya abubuwan da ya shirya domin samun nasara a mulkinsa.

Ya yi kira ga shugaban kasa da ya sake fitowa takara a 2019.

Ya kara da cewa dole ne fa gwamnatin nan ta yi nasara ko domin mu da muka amfana da farinjinin Buhari.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: