Friday, 17 March 2017

Musha Dariya: Duk Buhariyya Ce So Kakeyi Muyi Fada

Wani magidanci ne yana hira da matarsa sai yacemata:
Honey gaskiya budurwata Aisha tana qaunata sosai. Matar tace masa, Gaskiya Aisha budurwarka ta burgeni.

Maigidan nata yace, Rannan fa har cemin tayi honey na yadace muje Wellcare domin muyi siyayyar kayayyaki. Sai matar tace gaskiya ta burgeni.

Sai mai Gidan nata yace, Jiya fa har cemin tayi honey I love u very very much. Sai matar tace masa, Gaskiya budurwarka tana sonka.

Sai mai Gidan yace dazu kuwa tacemun, Ina my son (danki)? Kinsan tafiki Qaunarsa. Sai matar tace gaskiya ta burgeni.

Qarshe dai sai mai gidan yacemata, Wai ke Sadiya babu abinda yake bata miki rai ne?
Budar bakin matar sai tace, Eh babu abinda zance, ai na ganeka:
Duk BUHARIYYA ce, So kakeyi muyi fada ka korani gida, Ba inda zani

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: