Wednesday, 27 September 2017

Dokokin Hukunta Masu Aikata Laifukan Zabe A Nijeriya!

Hakika matakin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC) ta dauka, cewa zata fara gurfanar da dukkan wadanda aka samu da laifin saba ka’idojin zabe a kasar, abin yabo ne, sannan kuma wata alama ce dake nuna cewa an fara diga dan ba, wajen tsaftace harkokin zabuka a Nijeriya.

Shugaban Hukumar Zabe na Kasa, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka, sannan kuma ya tabbatar da cewa hukumar ta samu nasarar gano laifuka har 61 wadanda za a iya gurfanar da wanda ya saba su, tun daga shekarar 2015. Haka nan kuma adadin na iya karuwa fiye da haka, biyo bayan irin shiriritar da aka samu a zabukan cike gurbi na Jihar Ribas a Watan Disambar 2016 a mafi yawan wuraren kada kuri’a.

Har ila yau, Sugaban Hukumar ya tabbatar da cewa sun sake samun wasu karin laifukan saba ka’idojin zabe har guda 120 daga Rundunar ‘Yan Sanda ta kasa.

Yakan kasance a kasar irin Nijeriya a samu hukumomin kasa masu zaman kansu da suke fara bijerewa ko yin watsi da hatta tsare-tsare ko dokokin da hukumar ta kafu akansu. Wannan yunkuri da Hukumar Zabe na wannan lokacin ta yi, na gurfanar da dukkan wanda aka samu da laifin saba dokokin zaben koda kuwa ma’aikatanta ne, domin kawai bukatar kashin kai, babban abin alfahari da ci gaba ne.

Kuma hakika lokaci ya yi ga masu aikata laifukan zabe a kasar, zasu fara dandana kudarsu, sakamakon irin damar da suka samu wajen aikata wadannan ta’addanci da kuma canza sakamakon zabe da sauransu.

Haka zalika kuma ya dace a jinjina wa Farfesa Yakubu bisa wannan yunkuri wanda ya kasance shine irinsa na farko a tarihin kasar nan, ta yadda hukumar zabe zaka zama ba kawai kokarin baiwa kanta kariya ba, har ma da daukar babban matakin kawo karshen tozarta sha’anin zabuka ga Wadanda suke amfana da hakan ta hanyar samun makudan kudade daga gurbatattun ‘yan siyasa, ba kuma kawai su fuskanci shari’a ba, har ma da kunyatar da su ga jama’a bisa miyagun ayyukan nasu.

Bugu da kari ma a yanzu haka tuni hukumar ta kafa wani sabon kwamiti, domin bincike kan almunhanar da ake zargin wasu jami’an hukumar su fiye da 200 da suka karbi rashawar da ta kai kimanin naira bilyan 23 a zabukan 2015 da suka gabata.

Kuma abu ne sananne cewa gurbatattun ‘yan siyasar kasar nan, kan iya biyan koda nawa ne ga jami’an hukumar zabe, domin tabbatar da cewa an canza sakamakon zuwa ga yadda suke bukata. Da wannan dalili ne ma, hukumar zaben ta lashi takobin ganin ta bankado dukkan wadanda ke da hannu cikin badakalar zaben, ta hanyar haska babbar tocila don tabbatar da cewa babu wanda ya sha cikinsu.

A ra’ayinmu, wannan wata hanya ce da hukumar ta dauka wanda zai kai ga yin tarnaki ga jami’an hukumar zaben, wajen saurin amincewa da bukatun ‘yan siyasa don hargitsa harkokin zabukan kasar anan gaba. Haka nan kuma hatta su kan su gurbatattun ‘yan siyasar da suka kawo cikas a sha’anin zaben sun fuskanci hukuncin da ya dace.

Haka zalika hukumar zaben na bukatar ta waiwayi rahotannin saba ka’idojin zabe wadanda Hukumar Kare Hakkin Dan’Adam (NHRC) ta ruwaito, inda ta bankado wasu miyagun ‘yan siyasar kasar da hadin bakin wasu jami’an hukumar zabe da kuma ofishin Babban Lauyan Gwamnati don tabbatar cewa an gurfanar da su gaban kuliya.

Baya ga wannan, yana da kyau hukumar ta waiwayi rigingimun zabukan baya, wadanda suka hada rikicin zaben Jihar Ribas na watan Disambar bara, da zaben cike gurbi a watan Afirilun bara a Karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano, wadanda za su zama hujja da ayyukan daidaikun al’umma wajen dakile nagartar zabuka don bukatar kashin kai.

Hakika rikicin zaben Jihar Ribar ya fi zama zakaran gwajin dafi, wajen bayyana miyagun laifukan zabe, dake bukatar hukumar ta yi ruwa da tsaki wajen bincikowa tare da gurafanar da dukkan wadanda aka samu da laifuka don zama darasi ga na baya.

Sannan a karshe yana da matukar kyau ga hukumar ta sanya harkokin jam’iyyu wajen kula da adalcin tsaida ‘yan takarar da al’umma ke so, samar da kyakkywan yanayi gabanin fara zabe da kuma isar kayayyakin zabe ko’ina don kaucewa hargowa da rudanin zabe. Don haka, Farfesa Mahmud Yakubu na hukumar zabe, na bukatar goyan bayan dukkan al’ummar Nijeriya don ba shi kwarin gwiwar aiwatar da gudurorin zabukan kasar anan gaba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: