A yayin da majalisar tarayyar ta ci gaba da zaman taro a yau talata, 26 ga watan Satumba bayan hutun watannin biyu, majalisar dattijai ta yi kira ga ma'aikatar albarkatun ruwa ta tarayya, don fara yashe kogin Binuwe da Neja don kaucewa hadarin ambaliyar ruwa.
Za a iya tuna cewa, yawancin al'ummomi da jihohi a Najeriya kwanan nan sun fuskanci matsaloli daban-daban, sakamakon ambaliyar ruwa wanda ke haifar da babbar hasara ga rayuka da dukiyoyi.
Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a cikin motsi da sanata Yahaya Abdullahi mai wai wakiltar Kebbi ta arewa da kuma sanata Aliyu Sabi Abdullahi daga Nejar ta arewa suka yi, majalisar dattijai ta bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi su saka dokar yin amfani da ƙasa da tsarin muhalli, don tabbatar da tsarin tsabtace magudanar ruwa.
"Ambaliyar ruwa na kwanan nan da kuma barnar dukiyoyin al’umma da ke tsakanin kogunan Neja da Binuwai da kuma yankunan da ke iyaka da su, sun kasance masu matukar damuwa, suna kusan kusan kowace shekara a lokacin damina tare da mummunar barna a wurare da dama da kuma yankunan karamar hukumar na jihohin Kebbi, Neja, Kogi, Kwara, Imo da Binuwai", inji sanata Abdullahi.
Don kauce wa cututtuka kamar kwalara, majalisar dattijai ta bukaci hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta gaggauta shirya agaji da taimakon likita a wuraren da ambaliyar ta shafa.

0 comments: