Wata rana wani malami yana zaune tare da almajiransa ana ta hira, sai ya tambayesu “anya kuwa suna son matayensu?” Gaba daya suka amsa da “kwarai kuwa” Allah ya gafarta Malam.
Sai Malam ya sake cewa “Yaushe rabon da kowannenku ya furtawa matarsa cewa yana sonta?” Misali ya ce mata “I love you” ma’ana ina sonki. To, anan ne suka fara bada amsa, wani ya ce kusan wata daya kenan, wani ya ce fiye da shekara, wani ya ce ba zai iya tunawa ba, da sauransu.
Daga nan Malam ya umarci kowa ya rubuta sakon <I love you> ta wayar salula ya aikawa matarsa, domin ganin wadanne irin amsoshi za su samu. Cikin kankanin lokaci sai ga amsoshi sun fara zuwa daga wajen matayen kamar haka:

- Mhmm da kenan banda yanzu…..
- Maganar auren naka ta rushe kenan?
- Kana son na baka aron kudi kenan?
- A mafarki kenan
- Tab! Allah ya kamaka, bari ka dawo ka fadamin wadda ka je aikama wannan sako
- Hmmm me kake nufi? Wannan karon ba zan yarda ba.
- Waye wannan?
- Wata sabuwa!
- Yau kuma?
- Hmm! Munafiki. Wallahi ban hakura da abin da kamin ba….
- I love you din banza…..
- Na fada maka, ka daina shaye shaye……
0 comments: