Wednesday, 1 March 2017

Musha Dariya: Wayafi Sakarci Dan Fulani Ko Baffansa?

Wani Bafulatani ne kullum sai an yi masa sata a gonarsa. Abu fa ya dami Bafulatani, sai wata rana ya ce bari na buya ko zan kama barawon.
Can kawai sai ga barawo ya zo ya debi amfanin gona ya saba a kafada zai tafi. Sai Bafillace ya kama shi ya ce “Yau dubunka ya shika. Lalle yau akoi lugude a rugga.”

Ya tusa keyar barawo suka nufi ruga. Suna cikin tafiya sai barawon ya ce ya manta takalminsa a gona, a saboda haka sai dai su koma su dauko.
Sai dan fulani ya ce “Shabbijan, sai da muka jo nan sannan za ka she mu koma gona???” Ya ci gaba da cewa “Ni ba zan koma ba, sai dai ka yi gudu ka je ka dauko ina jiranka”

Barawo ya yunkara zai sauke kayan sati don ya koma gona, sai Dan fillo ya ce ” Kai wa ka ke nufin zai maka gadin kayan satarka?? Ai da su za ka je ka dawo, ina jiranka, Wallahi kuma kar ka zauna wasa”
Shiru, shiru barawo bai dawo ba, sai Dan fulani ya tafi gida, ya je yana bawa baffansa labari, sai baffan nasa
ya ce, “Amma kai akwai sakarai, maimakon ka she ya tsaya ka je kadauko masa.”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: